An kusa bada umarnin hada NIN da BVN na asusun bankin 'yan Najeriya, Dr Pantami
- A kokarin gwamnatin tarayya na ganin ta hade bayanan 'yan Najeriya waje daya, za a hada NIN da asusun banki
- Hukumar NIMC za ta bada umarnin fara hada lambobin NIN da asusun bankin 'yan Najeriya
- A baya kuwa, an bayyana yiyuwar maye gurbin BVN da NIN don samun matsaya daya
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Dokta Isa Pantami a ranar Laraba ya ce Gwamnatin Tarayya za ta sanar da lokaci ga 'yan Nijeriya don hade Lambobin Shaida na Kasa (NINs) da asusun banki, The Nation ta ruwaito.
Pantami, wanda ya zanta da manema labarai na gidan gwamnati a karshen taron Majalisar zartarwa ta Tarayya (FEC), ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da jadawalin yadda za a hada NIN da asusun banki.
Ministan ya kuma ce NIN za ta maye gurbin lambar Tabbatar da Bankin (BVN) saboda dokar ba ta da goyon baya.
KU KARANTA: Filayen jirgin saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma
A baya, Dr Pantami ya bada umarnin hade layukan waya da lambobin NIN, wanda ya jawo cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya lura da yadda aikin na NIMC ya ke tafiya da kuma kankanin lokaci da ya bayar.
Bayan korafin da 'yan Najeriya suka yi game da lokacin bayar da umarnin wanda ya kai ga 'yan kasa suka yi cincirindo a wasu cibiyoyin rajista na Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) a duk fadin kasar an kara wa'adin hadewar.
Hakazalika, hukumar ta NIMC ta baiwa kamfanoni masu zaman kansu damar yin rajistar NIN.
KU KARANTA: IPPIS zamba ne, gwamnati ta yaudare mu ne kawai, inji wani shugaban NASU
A wani labarin, Shugaban majalisar dattijai, Yahaya Abdullahi, ya ce zauren dattijai zai tattauna kan matsalar rikicin makiyaya Fulani a duk fadin kasar a ranar Talata, jaridar Punch ta ruwaito.
Abdullahi, wanda ya zanta da manema labarai a ofishinsa, ya ce mataimakinsa wanda ke wakiltar Ondo ta Arewa a Majalisar Dattawa, Farfesa Ajayi Boroffice, zai gabatar da kudiri kan batun.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng