Buhun Siminti Zai Yi Arha, Shugaba Tinubu Ya Aike da Saƙon Farashi Ga Dangote, BUA da Wasu Kamfanoni

Buhun Siminti Zai Yi Arha, Shugaba Tinubu Ya Aike da Saƙon Farashi Ga Dangote, BUA da Wasu Kamfanoni

  • Bola Ahmed Tinubu ya umarci kamfanonin da ke samar da siminti su koma asalin farashin siminti na baya kafin faɗuwar Naira
  • Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce Tinubu ya bai wa kamfanonin wannan umarni ne yayin ganawarsu a makon da ya wuce a Villa
  • Ya kuma yabawa kamfanin BUA bisa kammala aikin layi na 5 na samar da siminti yayin da ya kai ziyara kamfanin a Sakkwato

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci kamfanonin da ke samar da siminti a Najeriya da su koma asalin farashin da suke siyar da kayansu a baya.

Ministan ayyuka, David Umahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan ya duba masana’antar simintin BUA da ke Sokoto ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Binance: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya goyi bayan matakin da Shugaba Tinubu ya dauka

Tinubu ya buƙaci a maida asalin farashin siminti.
Tsadar Siminti: Shugaba Tinubu Ya Umarci Dangote, BUA da Wasu Su Koma Tsohon Farashi Hoto: Dangote Group, BUA
Asali: UGC

Umahi ya ce yayin ganawar da shugaban ƙasa ya yi da masu masana'antun siminti, ya umarci su koma kan asalin farashin siminti na baya, Daily Truat ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce:

"Ina jan hankalinsu da ƙara musu kwarin guiwar su bi umarnin shugaban ƙasa domin mu samu ikon cimma kudirin samar da gidaje da kuma tsarin titunan kankare da (Tinubu) ya ɓullo da shi."

Sanata Umahi ya yabawa kamfanin BUA

Bugu da ƙari, Umahi ya yabawa kamfanin samar da simintin BUA bisa nasarar da ya samu ta kammala aikin layin haɗa siminti na 5.

Umahi ya ci gaba da cewa:

"Lokacin da shugaban wannan kamfani ya ziyarci shugaban ƙasa a makon jiya, ya bada tabbacin cewa nan ba da jimawa ba layin haɗa simintinsa na 5 zai fara aiki.
"Kuma a wannan ziyara da ja kawo yau na gani da ido na cewa layin na 5 duk da ana dakon zuwa a kaddamar da shi, ya riga ya fara aiki."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya keɓe minista 1, ya yaba masa kan yadda ya share hawayen ƴan Najeriya

Bayan haka kuma ya yabawa mahukuntan kamfanin bisa tabbatar da tsafta a daukacin harabar kamfanin.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya na shirin fara aikin titi mai tsawon kilomita 372 daga Zaria zuwa jihar Sokoto, rahoton The Nation.

Shugaba Tinubu ya fusata da zanga-zangar NLC

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya caccaki kungiyar kwadago ta ƙasa NLC kan zanga-zangar da ta yi domin nuna adawa da tsadar rayuwa da yunwa

Shugaban ya ce ba zai yiwu NLC ta yaƙi gwamnatin da ba ta wuce wata 9 ba, yana mai cewa ba su ne kaɗai ke magana da muryar ƴan Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel