A Fadi Illar da Kiripto Ke Yi Wa Tattalin Arziki Yayin da Aka kama Shugabannin Binance, Za a Haramta

A Fadi Illar da Kiripto Ke Yi Wa Tattalin Arziki Yayin da Aka kama Shugabannin Binance, Za a Haramta

  • A kokarinta na dakile harkar Kirpto a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta tsare shugabannin Binance a birnin Tarayya Abuja
  • Wannan na zuwa ne bayan illar da Kiripto ya ke yi wa tattalin arzikin kasar wanda ke kawo cikas ga CBN na shirin inganta tattalin arziki
  • Haidmin Tinubu, Bayo Onanuga ya ce idan har ba a dakatar da Kiripto ba to tabbas za a samu babbar matsala a kasar na tattalin arziki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hadimin Shugaba Tinubu ya bayyana irin illar da Kiripto ke yi wa tattalin arzikin Najeriya a yanzu.

Bayo Onanuga ya ce idan har ba a dakatar da Kiripto ba to tabbas za a samu babbar matsala kuma za ta durkusar da tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Babban illar da Kiripto ke yi wa tattalin arzikin Najeriya
Gwamnati na daukar matakan dakile Kiripto a Najeriya. Hoto: @officialABAT, @binance.
Asali: UGC

Menene hadimin Tinubu ke cewa kan Binance?

Onanuga ya bayyana haka ne yayin hira da gidan takabijin na Channels inda ya ce akwai wasu yanar gizo na Kiripto da ke yanke farashin dala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Idan har bamu dauki mataki kan Binance ba, za ta durkusar da tattalin arzikin kasar gaba daya, su suke saka farashin dala wanda hakan matsala ne.
“Muna da masu mana zagon kasa, kalli yadda Binance ke lalata arzikin kasar nan, dole ne gwamnati ta dauki mataki kan haka.
“Wasu su na zaune wurin amfani da kafafen tare da saka farashin yadda suke so inda suka kwace abin da ya kamata CBN ne ke yi.”

Dalilin kama shugabannin Binance

Wannan na zuwa yayin da Gwamnatin Tarayya ke tunanin haramta Kiripto a kasar saboda illar da take yi wa tattalin arzikin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi alawus, bayanai sun fito

Har ila yau, hukumomi a Najeriya sun tsare manyan shugabannin Binance guda biyua kokarin dakile Kiripto a kasar.

Shugabannin Binance sun diro Najeriya ne bayan kokarin gwamnatin na dakatar da harkar amma sai aka kama su a ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro.

Wannan kokarin dakile Kiripto na zuwa ne bayan kirkirar wasu yanar gizo wanda ya zama barazana ga tattalin arzikin kasar da kuma karancin dalar.

An daure mai kamfanin Kirpto

Kun ji cewa kotu ta ta daure wani mai kamfanin Kiripto, Faruk Fatih Ozer shekaru dubu 11 a gidan kaso kan wasu zarge-zarge.

Ana zargin Fatih da kirkirar kamfanin Kiripto wanda ya ke amfani da shi wurin damfarar mutane biliyoyin kudade

Asali: Legit.ng

Online view pixel