Arewa Ta Samu Karuwa Bayan Amincewa da Jiharta a Cikin Jihohi Masu Arzikin Mai, Bayanai Sun Fito

Arewa Ta Samu Karuwa Bayan Amincewa da Jiharta a Cikin Jihohi Masu Arzikin Mai, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da aka yi zazzafar muhawara kan kasancewar jihar Kogi daga cikin jihohi masu arziki, Majalisa ta amince da bukatar
  • Majalisar ta ayyana jihar daga cikin jihohi masu arzikin man fetur tare da samun kaso 13 daga kudaden shiga na man
  • Majalisar ta tabbatar da haka ne a zamanta a jiya Alhamis 29 ga watan Faburairu bayan Sanata Jibrin Echocho ya gabatar da kudirin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Majalisar Dattawa ta ayyana jihar Kogi a Arewacin Najeriya daga cikin jihohi masu arzikin man fetur a kasar.

Majalisar ta tabbatar da haka ne a zamanta a jiya Alhamis 29 ga watan Faburairu inda ta ce za ta na samun kaso 13 daga kudaden shigar man.

Kara karanta wannan

Rikicin majalisa: 'Yan majalisa da aka dakatar sun shiga matsala, sun nemi alfarma 1

Majalisa ta amince da bukatar jihar Arewa kasancewa cikin jihohi masu arzikin mai
Majalisa ta ayyana Kogi daga cikin masu arzikin man fetur. Hoto: Hoto: NASS TV.
Asali: Facebook

Wane mataki Majalisar ta dauka kan jihar Kogi?

Wannan na zuwa ne bayan kudirin da dan Majalisar daga Kogi ta Gabas, Sanata Jibrin Isa Echocho ya gabatar yayin zamanta, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan zazzafar muhawara da aka yi a Majalisar inda Sanata Tony Nwoye ya ke kalubalantar jihar kan kasancewa cikin masu arzikin.

Echocho yayin zaman Majalisar ya gabatar da kudiri inda ya ke tabbatar da jihar a cikin masu arzikin man da samun kaso 13 daga kudaden man.

Martanin dan Majalisar jihar Kogi

Ya ce:

“Ina bukatar Majalisar da ta tabbatar da Kogi a matsayin jiha mai arzikin man fetur da samun kaso 13 kamar yadda kundin tsarin mulki ya tabbatar tun watan Oktoban 2023.”

- Sanata Jibrin Isa Echocho

Majalisar bayan muhawarar kan lamarin, ta tabbatar da Kogi a matsayin jihar mai arzikin man fetur da samun kaso 13, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

A fadi illar da Kiripto ke yi wa tattalin arziki yayin da aka cafke shugabannin Binance, za a haramta

Har ila yau, Majalisar ta ba da shawarar daukar mutane 10 aikin dan sanda a ko wace karamar hukuma a Najeriya.

Majalisar ta ba da umarni ne zuwa ga hukumar jin dadin ‘yan sanda don inganta tsaron kasar da ya tabarbare.

Majalisa ta ki amince da tsarin Tinubu

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta ki amincewa da karin kudin wutar lantarki a Najeriya inda ta ce bai kamata a yanzu ba.

Majalisar ta aike ta wannan sako ne ga Gwamnatin Tarayya da ke kokarin cire tallafin wutar lantarki a kasar saboda basuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.