Majalisar Dattawa Ta Bada Umarnin a Ɗauki Ƴan Sanda 10 a Kowace Ƙaramar Hukuma, Ta Faɗi Dalili

Majalisar Dattawa Ta Bada Umarnin a Ɗauki Ƴan Sanda 10 a Kowace Ƙaramar Hukuma, Ta Faɗi Dalili

  • Majalisar dattawa ta umarci mahukunta su ɗauki jami'an ƴan sanda 10 a kowace ƙaramar hukuma daga cikin 774 da ake da su a Najeriya
  • Wannan ya biyo bayan kudirin da Sanata Emmanuel Udende Memga daga jihar Benuwai ya gabatar kan buƙatar bin ƙa'idodji
  • Majalisa ta umarci kwamitocinta guda biyu su tabbata waɗanda umarnin ya shafa sun yi biyayya yadda ya kamata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta bada umarnin a ɗauki sabbin ƴan sanda 10 a kowace ƙaramar hukuma daga cikin ƙananan hukumomi 774 na Najeriya.

Majalisar ta aike da wannan umarni ne ga hukumar kula da jin daɗin ƴan sanda da kuma rundunar ƴan sanda ta ƙasa ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, 2024.

Kara karanta wannan

Binance: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya goyi bayan matakin da Shugaba Tinubu ya dauka

Majalisa ta umarci a ɗauki yan sanda 10 a kowace ƙaramar hukuma.
Majalisa Ta Umarci Rundunar Ƴan Sanda Ta Dauki Mutum 10 Aiki a Kowace Karamar hukuma Hoto: NGRSenate, PoliceNG
Asali: Twitter

A cewar majalisar wannan umarnin ya shiga cikin wani ɓangare na ɗaukar sabbin ƴan sandan da ake yi duk shekara, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An cimma wannan matsaya ne biyo bayan kudirin da Sanata Emmanuel Udende Memga, mai wakiltar Benuwai ta Arewa maso Gabas ya gabatar.

Kudirin dai ya nuna bukatar hukumar jin daɗin ƴan sanda da rundunar ƴan sanda su bi ƙa'idar da ke akwai wajen ɗaukar sabbin jami'ai aikin ɗan sanda.

Bayan haka kuma majalisar dattawan ta umarci kwamitin kula da harkokin ƴan sanda da kwamitin bin doka da oda su tabbatar an yi biyayya ga wannan umarni.

Wane kudiri Sanata Barau ya kai majalisa?

Wannan na zuwa ne yayin da kudirin kirkiro ofishin kasafin kuɗi da bincike a majalisar tarayya ya tsallaka zuwa matakin karatu na biyu a majalisar yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Dandutse: Ƴan bindiga sun kashe babban soja da wasu jami'ai biyu, sun tafka ɓarna kan bayin Allah

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ne ya ɗauki nauyin gabatar da kudirin kafa wannan ofishi.

Idan har ya tsallake ya zama doka, ofishin zai zama madogarar majalisar dokokin ta ƙasa wajen yanke yadda kasafin kuɗinta zai kasance ba tare da nuna ɓangaranci ba.

Kakakin ƴan sandan Gombe ya shiga daga ciki

A wani rahoton kuma Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Gombe, Mahid Abubakar, ya shiga daga ciki a ranar Asabar, 24 ga watan Fabrairu.

Abubakar wanda ya yi wuff da sahibarsa mai suna Nafisa, ya ce tun a 2010 ya fara ganinta kuma nan take ya kamu da sonta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel