Rikicin Majalisa: 'Yan Majalisa da Aka Dakatar Sun Shiga Matsala, Sun Nemi Alfarma 1

Rikicin Majalisa: 'Yan Majalisa da Aka Dakatar Sun Shiga Matsala, Sun Nemi Alfarma 1

  • Mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara da aka dakatar sun ruga zuwa wajen Shugaban kasa Bola Tinubu domin neman mafita
  • 'Yan majalisar sun kuma yi kira ga ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniya da kungiyar ECOWAS akan su taimaka wajen ceto dimokradiyyar jihar daga fadawa halaka
  • Tun farko dai an dalkatar da su ne kan wasu dalilai da suka hada da zargin cin mutuncin majalisa, gudanar da zama ba bisa ka’ida ba da kuma rashin da’a

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Zamfara - 'Yan majalisar dokokin jihar Zamfara da aka dakatar sun bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu da majalisar dokokin tarayya da su sanya baki a rikicin da ya dabaibaye zauren.

An yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da dakatattun 'yan majalisar suka yi a Zaria, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dura kan 'yan Crypto, ta kakaba wa Binance tarar dala biliyan 10

Majalisar dokokin jihar Zamfara
Rikicin Majalisa: 'Yan Majalisa da Aka Dakatar Sun Shiga Matsala, Sun Nemi Alfarma 1 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Dan majalisa mai wakiltar Gumi 1, Bashir Aliyu Gumi, ya kuma yi kira ga ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniya da kungiyar ECOWAS da su ceci dimokaradiyya daga hatsari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa aka dakatar da 'yan majalisa?

Idan za ku tuna, a makon jiya ne aka sanar da Gumi a matsayin kakakin majalisa na wucin gadi, bayan wasu 'yan majalisa sun ce an tsige kakakin majalisar, Bilyaminu Moriki.

Sai dai kuma, a yayin zamanta na ranar Litinin, majalisar ta sanar da dakatar da Gumi tare da wasu 'yan majalisa bakwai bisa zargin cin mutuncin majalisa, hada baki, gudanar da zama ba bisa ka’ida ba, barna, da kuma rashin da’a.

Gumi, wanda yake tare da ‘yan majalisa 11, ciki har da wadanda dakatarwar ba ta shafa ba, ya ce manufarsu ba ta da alaka da siyasa, illa dai kokarin ceto dimokuradiyya da matsalar tsaro da ya addabi jihar.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata, sun fito zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga a jihar Arewa

Daily Trust ta kuma ruwaito cewa Nasir Mukhtar, 'dan majalisa mai wakiltar Kauran Namoda ta Arewa, wanda baya cikin 'yan majalisar da aka dakatar, ya ce ci gaban ya yi illa ba kadan ba kuma kuma yana iya lalata dimokuradiyyar jihar.

'Yan bindiga sun sace masallata a Zamfara

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu masallata a ɗaya daga cikin masallatan garin Tsafe hedikwatar ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin mai suna Garba ya shaidawa jaridar The Punch cewa ƴan bindigan sun mamaye masallacin ne da misalin ƙarfe 5:00 na safiyar ranar Alhamis a lokacin da mutanen ke shirin fara sallar Asuba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel