Majalisar Dattawa Ta Amince da Bukatar Tinubu Na Korar Shugaban FCCP

Majalisar Dattawa Ta Amince da Bukatar Tinubu Na Korar Shugaban FCCP

  • Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na korar shugaban hukumar FCCP, Babatunde Irukera
  • Shugaban majalisar dattawa, GodsWill Akpabio ne ya karanta wasikar da Tinubu ya aike wa majalisar ta korar Irukera a ranar Laraba
  • A bisa dokar FCCPC, shugaban kasa na bukatar amincewar majalisar dokokin kasar don korar babban mataimakin shugaban hukumar

Abuja - Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na korar shugaban hukumar kula da gasar kasuwanci da kare masu sayen kayayyaki ta tarayya, Babatunde Irukera.

Tinubu a wata wasika da shugaban majalisar dattawa, GodsWill Akpabio ya karanta a zauren majalisar a ranar Laraba, ya ce ya bukaci a kori Irukere ne bisa rashin kwarewar aiki.

Majalisar dattawa ta amince da bukatar korar shugaban hukumar FCCP
Majalisar dattawa ta amince da bukatar korar shugaban hukumar FCCP, Mr Babatunde Irukera. Hoto: @fccpcnigeria/@NGRSenate
Asali: Twitter

Majalisar ta kad'a kuri'a, mafi rinjaye sun yarda

A bisa dokar FCCPC, shugaban kasa na bukatar amincewar majalisar dokokin kasar don korar babban mataimakin shugaban hukumar, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa na kori Irukere a matsayin shugaban FCCPC, Tinubu ya fadawa majalisar dattawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, a watan Janairu, Tinubu ya kori Irukera da kuma shugaba na hukumar kamfanonin jama'a, Mista Alexander Okoh.

Bayan tattaunawa, an gabatar da bukatar a kada kuri’a a inda masu kiran 'ayes' suka fi rinjaye wanda kuma ya sa shugaban majalisar dattawa ya buga sanda don tabbatar da bukatar.

Dalilin da ya sa na kori Irukere a matsayin shugaban FCCPC - Tinubu

Tun da fari, Legit ta ruwaito shugaban kasa Bola Tinubu ya ce ya kori Babatunde Irukere daga matsayin shugaban hukumar FCCPC sakamakon rashin kwarewarsa wajen gudanar da ayyukan ofishinsa.

Shugaba Tinubu ya ce ya dace a sake fasaltamuhimman hukumomi na gwamnatin tarayya don kara karfafa aikin su wanda ya hada da korar wadanda ba su cancanta ba.

Mai magana da yawun Tinubu, Ajure Ngelale ne ya aika wa majalisar wata wasika ta neman amincewar tsige Irukera tun a watan Janairu.

Kara karanta wannan

Kamfanin Ajaokuta: Majalisa za ta binciki gwamnatin Yar'adua, Jonathan da Buhari kan fitar da $496m

Korar Irukera ya jawo cece-kuce

Bayan sanar da tsige Irukera daga kujerarsa kuma tsigewa ta nan take, babban lauya, Femi Falana ya ce matakin ya saba da dokar da ta kafa hukumar FCCPC.

Femi Falana ya ce bai kamata nan take a tsige Irukera ba, har sai majalisar dattawa ta amince da bukatar tukunna.

Haka kuma Falana ya zargi Tinubu da yin amfani da kalmar 'Tsigewa' a takardar dakatar da Irukera, wadda ya ce kalmar ba ta dace ba tunda ba wai an sallame shi don ya aikata wani laifi ba ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel