Majalisa Ta Daga Yatsa Ga Tinubu Kan Cire Tallafin Wutar Lantarki, Ta Fadi Lokacin da Ya Kamata

Majalisa Ta Daga Yatsa Ga Tinubu Kan Cire Tallafin Wutar Lantarki, Ta Fadi Lokacin da Ya Kamata

  • Yayin da ake kokarin cire tallafin wutar lantarki a Najeriya, Majalisar Dattawa ta kekashe ta ce ba zai yi yu ba a halin yanzu
  • Majalisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta janye kudirinta na cire tallafin wutar lantarki ganin irin halin da ake ciki
  • Sanata Aminu Iya Abbas da ke wakiltar Adamawa ta Tsakiya shi ya gabatar da kudirin a gaban Majalisar a yau Laraba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta janye kudirin cire tallafin wutar lantarki.

Majalisar ta ce ganin yadda ake cikin wani hali a kasar bai kamata a bijiro da maganar cire tallafi a wutar lantarki ba.

Kara karanta wannan

Sanatoci za su kafa kwamitin binciken Buhari kan bashin N30tr da ya ci a CBN

Majalisa ta gargadi Tinubu kan cire tallafin wutar lantarki
Majalisar Dattawa ta yi gargadi kan cire tallafin wutar lantarki. Hoto: Godswill Akpabio, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene Majalisar ke cewa kan wutar lantarki?

Wannan ya biyo bayan kudirin da Majalisar ta kawo na cewa dole a bar tallafin wutar lantarkin zuwa gaba, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Aminu Iya Abbas da ke wakiltar Adamawa ta Tsakiya shi ya gabatar da kudirin a gaban Majalisar a yau Laraba 21 ga watan Faburairu.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnati ta koka kan basukan da ke bangaren wutar lantarkin inda ta ce ba za ta iya ci gaba da biya tallafin ba.

Dalilin shirin gwamnati na cire tallafin wutar lantarki

Abbas ya ce abin takaici ne yadda ake kokarin kara kudin wutar lantarki duk da mummunan yanayi da ake ciki.

Sanatan ya kara da cewa kamfanonin na karbar kudaden wutar lantarki da yawa a hannu 'yan kasa ba tare da ba su isasshen wuta ba yayin ba su inganta komai ba a kamfanin.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun lalubo yadda Gwamnatin Buhari ta haddasa asarar Naira tiriliyan 17

Ya kara da cewa mutanen unguwa ne ke sauya injunan ba da wuta duk lokacin da ta baci duk da biyan makudan kudade da suke yi.

Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu shi ya bayyana haka a Abuja inda ya ce dole Najeriya ta dauki mataki kan haka, kamar yadda Thisday ta tattaro.

A cewarsa:

“Ya na da wahala Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da biyan tallafin wutar lantarki.”

Adelabu ya ce basukan da ke tattare da kamfanonin samar da wutar lantarkin ya yi yawa wanda haka ne kadai hanya mafi sauki.

'Yan Majalisa na tare da 'yan kasa

A baya, mun ruwaito muku cewa Majalisar Tarayya ta ce za ta yi duk mai yiyuwa don dakile shirin cire tallafin wutar lantarki.

Majalisar ta ce kwata-kwata ba sa jin dadin abin da ke faruwa musamman halin kunci da ake ciki na mawuyacin hali.

Wannan na zuwa ne yayin da Gwamnatin Tarayya ke kokarin cire tallafin wutar lantarki bayan cire na man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel