Tsadar Rayuwa: Ba Laifin Tinubu Ba Ne, Igboho Ya Yi Martani Kan Kalaman Sarkin Musulmi

Tsadar Rayuwa: Ba Laifin Tinubu Ba Ne, Igboho Ya Yi Martani Kan Kalaman Sarkin Musulmi

  • Mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya yi martani kan maganar Sarkin Musulmi da ya ce akwai matsala a kasar
  • Igboho ya ce bai kamata a daura laifi a gwamnatin Tinubu da ta yi watanni takwas kacal ba a mulki inda ya ba a kawar da matsalar dare daya
  • Wannan martani na zuwa ne bayan Sultan ya gargadi hukumomi kan matsifar da ake fuskanta a kasar yayin da ake cikin halin kunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT Abuja - Yayin da ake fama da tsadar rayuwa da rashin tsaro, Mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya kare gwamnatin Tinubu.

Igboho ya fadawa Sultan Sa'ad Abubakar cewa matsalar tsaro ba za a iya dakile ta rana daya ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

Igboho ya yi martani kan kalaman Sarkin Musulmi
Sunday Igboho Ya Yi Martani Kan Kalaman Sarkin Musulmi. Hoto: Sa'ad Abubakar, Sunday Igboho.
Asali: Facebook

Wane martani Igbo ya yi ga Sarkin Musulmi?

Wannan martani na zuwa ne bayan Sultan ya gargadi hukumomi kan matsifar da ake fuskanta a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sultan ya ce an iso wani gaba da ba za su iya dakatar da matasa ba yayin da za su fito neman mafita a kasar.

Igboho ya yi martanin ne a jiya Alhamis 15 ga watan Faburairu a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar Vanguard.

Igboho ya ce ba laifin Tinubu ba ne

Mai fafutukar ya roki a bai wa Tinubu lokaci ya kawo karshen matsalar da ke ciki a tsare-tsaren da ya dauko.

Sunday ya ce tabbas maganar Sultan ta na kan hanya amma bai kamata a daura laifukan kan Tinubu ba, kamar yadda Premium Times ta tattaro.

Ya ce kwata-kwata watanni takwas kacal gwamnatin ta yi a kan mulki inda ta gaji wasu matsaloli a baya.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Tinubu ta jawo 'yan Najeriya na mutuwa saboda yunwa, in ji hadimin Atiku

Sultan ya fusata kan matsalar Najeriya

A baya, mun ruwaito cewa Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya gargadi hukumomi kan halin kunci da ake ciki a kasar na tsadar rayuwa.

Sultan ya koka kuma kan matsalar rashin tsaro da yunwa da kuma talauci da ake fama da shi.

Ya ce akwai mummunan hatsari da ke fuskantar Najeriya idan har ba a dauki matakin kare matsalolinta tsaro da talauci da aikin yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel