Sunday Igboho Ya Bayyana Abu 1 da Bai Kamata Tinubu Ya Manta da Shi Ba

Sunday Igboho Ya Bayyana Abu 1 da Bai Kamata Tinubu Ya Manta da Shi Ba

  • Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ce Shugaba Bola Tinubu na daukar matakan da ya cancanci a yaba masa ya kuma yi masa addu'ar samun lafiya
  • Dan fafutukar kasar Yarbawan ya bayyana cewa bai kamata Shugaban kasar ya manta cewa Yarbawa na shan wahala ba
  • Igboro ya jaddada cewar Tinubu ya fara yunkurin farfado da kasar zuwa mai inganci sannan ya nuna kwarin gwiwar cewa shugaban kasar zai yti shekaru takwas a mulki

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Dan fafutukar kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya jinjinawa Shugaban kasa Bola Tinubu kan daukar matakan da suka dace don farfado da Najeriya.

Kara karanta wannan

"Kada ku tsinewa shugabanninmu": Sarkin Musulmi ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Igboho ya ce Shugaban kasar na yin abubuwan da suka kamata da daukar matakan da suka dace a wata hira da gidan talbijin na Alaroye ta yanar gizo a karshen mako.

Sunday Igboro ya ce Tinubu na bisa kan hanya madaidaiciya
Sunday Igboro Ya Bayyana Abu 1 da Bai Kamata Tinubu Ya Manta Ba Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Sunday Igboro ya yi wa Shugaba Tinubu addu'a

Daga bisani, dan fafutukar ya yi wa Shugaba Tinubu addu'ar samun cikakken lafiya don ci gaba da kyawawan ayyukan da ya fara, yana mai cewa tsohon gwamnan na jihar Legas ya dauki hanyar farfado da kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Igboro ya bayyana cewa shugaban kasar ya nada manyan mukamai wanda ke nuna yana sane da abubuwan da ke kewaye da shi.

Sai dai kuma, Igboho ya bayyana cewa ya zama dole Shugaban kasar ya tuna cewa Yarbawa na shan wahala. Ya nuna kwarin gwiwar cewa za a sake zaben Shugaba Tinubu a 2027 kuma zai yi wa'adi biyu a mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana babban abin da ya ke mutunta Tinubu da shi bayan hukuncin Kotun Koli

Yarbawa na wahala, Igboro ga Tinubu

Dan fafutukar wanda yake haifaffen jihar Oyo ya nuna yakinin cewa Allah zai tallafawa shugaban kasar wajen farfado da kasar.

Igboro ya yi wa Tinubu addu'ar samun tsawon rai don ya sauya kasar don ta inganta.

Wani bangare na jawabin Igboho na cewa:

"Ina so Shugaba Tinubu ya tuna cewa Yarbawa na wahala. Shakka babu zai yi amfani da shekaru 8. Allah zai taimake sa a tsarin shugabanci. Allah zai ba shi tsawon rai don ya yi nasarar sauya kasar nan ta inganta."

Tinubu ya yi kus-kus da Fubara

A wani labarin, mun ji a baya cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na ganawar sirri yanzu haka da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Fubara ya isa fadar shugaban kasa da yammacin ranar Alhamis misalin karfe 5:35, sannan ya wuce ofishin shugaban kasa kai tsaye domin ganawar sirri, Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel