Gawarwaki Sun Fara Rubewa a Barikin Soja Bayan Matakin da Kamfanin Wuta Ya Dauka, an Fadi Dalili

Gawarwaki Sun Fara Rubewa a Barikin Soja Bayan Matakin da Kamfanin Wuta Ya Dauka, an Fadi Dalili

  • Rundunar sojin Najeriya ta koka kan yadda kamfanin wuta ya jefa su cikin duhu wanda ke neman jawo matsala a barikoki
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa gawarwaki sun fara rubewa a wurin adana gawarwakin a barikokin saboda rashin wuta
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wata ma'aikaciya a kamfanin samar da wutar lantarki kan lamarin basukan wutar a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tun bayan gargadi da kamfanin samar da wutar lantarki kan datse wutar barikin sojoji, abin ya fara tasiri kan gawarwaki.

Gawarwaki da ke wurin adana gawa a barikin sojoji sun fara rubewa sakamakon datse wutar lantarki da kamfanin ya yi.

Kara karanta wannan

Kwastam ta fara raba wa talakawan Najeriya kayan abinci da ta kwace, ta fadi ka'idojin cin gajiyar

Rundunar soji ta koka kan matsalar rubewar gawarwaki kan wani dalili
Rundunar sojin Najeriya ta nemi taimako kan yadda gawarwaki ke rubewa. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Facebook

Wane korafi rundunar ta yi?

Hafsan sojin Najeriya, Janar Taoreed Lagbaja shi ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara wurin Ministan makamashi, Adebayo Adelabu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lagbaja ya kai ziyarar ce don neman yadda za a shawo kan lamarin wanda ya jefa barikin a cikin mummunan duhu, cewar Daily Trust.

Idan ba a manta ba, Kamfanin samar da wutar a Abuja, AEDC ya yi gargadi ga ma’aikatu 83 kan su biya bashin biliyan 47 ko ya datse wutar.

Har ila yau, hatta fadar shugaban kasa ba ta tsira ba amma sai dai Shugaba Tinubu ya shiga lamarin bayan fitar da sanarwar inda ya umarci a biya basukan.

Yayin ziyarar, Lagbaja ya koka inda ya ce wasu barikokin sojoji sun kasance babu wuta tun a watan Janairu, cewar Vanguard.

Korafin hafsan sojin kan rashin wuta

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

A cewarsa:

“Bashin da ake binmu ya na cikin mitar wutar, don haka ko nawa muka saka ta na shanye shi nan take, gawarwaki a bakirin da muke ajiya a wurin adana gawarwaki duk sun fara rubewa kuma ‘yan uwansu sun fara korafi.”

Lagbaja ya kuma ce ba zai taba yiwuwa sojojin su iya hada wadannan makudan kudaden su biya ba kamar yadda aka yi a 2005.

A martaninsa, Adelabu ya bai wa rundunar tabbacin zama da kamfanin don neman hanyar samar da sauki.

Legit Hausa ta ji ta bakin wata ma'aikaciya a kamfanin samar da wutar lantarki kan lamarin.

Khadijah Abdullahi da ke aiki da JED a Gombe ta ce basukan da kamfanin ke bi ya wuce hankali.

Ta ce:

"Basukan ba iya barikokin sojoji ba ne kawai ko hukumomin gwamnati hatta unguwanni basukan sun wuce hankali.
"Dole ta saka kamfanin kara kudin wutar lantarki duk da ana maganar cire tallafin wutar a nan gaba.

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

"Shiyasa a wannan wata muke matsawa kowa sai ya kara kudin wuta fiye da yadda ya ke biya a baya."

An bukaci Tinubu ya cire tallafin wuta

Kun ji cewa Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa zai yi wahala a ci gaba da biyan tallafi a harkar wuta.

Adelabu ya bukaci Tinubu ya cire tallafin ganin yadda basukan ke karuwa wanda ya wuce hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel