Makiyan Kasa Ne, Sojoji Sun Fadi Matakin da Za Su Dauka Kan Masu Fatan Juyin Mulki, Akwai Dalili

Makiyan Kasa Ne, Sojoji Sun Fadi Matakin da Za Su Dauka Kan Masu Fatan Juyin Mulki, Akwai Dalili

  • Janar Christopher Musa ya gargadi masu kiran ayi juyin mulki inda ya ce kwata-kwata basu son Najeriya a zuciyarsu
  • Janar Musa ya ce irin wadannan mutane da ke fatan juyin mulki ba su da kishin kasa kuma makiyan Najeriya ce
  • Duk da tabbatar da kasar na cikin mawuyacin hali, amma ya kushe masu kiran juyin mulki inda ya ce hakan ba zai faruwa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce rundunar za ta dauki mataki kan masu addu’ar juyin mulki.

Janar Musa ya ce irin wadannan mutane da ke fatan juyin mulki ba su da kishin kasa kuma makiyan Najeriya ce.

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

Rundunar soji ta yi gargadi ga masu fatan juyin mulki
Sojoji sun gargadi masu kiran juyin mulki a Najeriya. Hoto: Gen. Christopher Musa.
Asali: Getty Images

Wane sako rundunar tsaron ta fitar?

Christopher ya ce rundunar za ta ci gaba da kare dimukradiyya a kasar kamar yadda ta saba kuma tabbas za ta kama masu wannan akidar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hafsan tsaron ya bayyana haka ne a jiya Laraba 21 ga watan Faburairu a Port Harcourt da ke Rivers, cewar The Nation.

Yayin da ya tabbatar da cewa kasar na cikin wani mawuyacin hali amma ya kushe masu kiran juyin mulki inda ya ce hakan ba zai taba faruwa ba.

Ya ce juyin mulkin ba shi ne mafita ba ko kadan inda ya ce Najeriya ta samu nasara a bangarori da dama dalilin dimukradiyya.

Gargadin rundunar ga 'yan Najeriya

A cewarsa:

“Duk wadanda ke kiran a yi juyin mulki ba su son Najeriya, muna kara tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da kare dimukradiyya.

Kara karanta wannan

Haka ba zai faru ba, Majalisa ta yi alkawari kan tsadar mai da wutar lantarki ga 'yan Najeriya

“Zamu kare dimukradiyya saboda ci gaban da aka samu a cikinta, duk wadanda ke kiran juyin mulki shaidanu ne kuma ba su son kasar da alkairi.
“Kuma su yi hankali saboda duk inda suke sai doka ta zakulo su, a dimukradiyya mun samu ci gaba duk da matsaloli saboda ba dole a samu komai dari bisa dari ba.”

Musa ya bukaci ‘yan kasa su yi hakuri da gwamnati da kuma ba ta goyon baya don inganta rayuwa da kunyata magauta, cewar Channels TV.

Sojoj sun bankado masana'antar kera makamai

Kun ji cewa, Dakarun sojin Najeriya sun gano wata boyayyiyar masana'antar kera makamai a kauyen Pakachi da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato.

Sojojin na gudanar da aikin share fage ne a wasu tsaunuka a lokacin da suka gano wurin da ake kera makamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel