Yadda Gwamnati Za Ta Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro a Cikin Awa Daya, Sheikh Daurawa
- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ba gwamnatin Najeriya satar amsa kan yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a cikin awa daya
- Sheikh Daurawa ya ce akwai bukatar shugaban kasar ya dauki tsattsauran mataki na kamo wadanda ake dangantasu da matsalar tsaron
- Daurawa ya jaddada cewa jami'an tsaron Najeriya na da karfi da kayan aikin magance matsalar tsaro idan har suka samu umarni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Nigeria ƙasa ce mai cike da ɗumbin arziki da kyawawan al'adu. Sai dai matsalar tsaro ta jefa al'umma cikin firgici da gaza samun abubuwan more rayuwa da dama.
Ganin yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta'azzara, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ba gwamnatin Shugaba Tinubu satar amsa, kan hanyar kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.
A mahangar malamin addinin, ma damar ana so a dawo da tsaro a Najeriya, to wajibi ne shugaban kasar ya dauki tsauraran matakai ko da kuwa ba za su yi wa wasu daɗi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wani faifan bidiyo da wani ma'abocin shafin X ya wallafa, an ji malamin addinin na cewa:
"Kuma wallahi tallahi in ana so a yi maganin ta'addanci a Najeriya, a awa ɗaya za a yi maganinsa."
Satar amsar da Daurawa ya ba gwamnati
1. Kamo mutanen da ake dangata su da tsaro
Da farko malamin ya ce akwai bukatar shugaban kasa ya ba da umarnin kamo duk wanda ake danganta shi da tsaro walau a mace ko a raye.
Ya ce:
"Shugaban kasa ya kira jami'an tsaro, ya ba su wa'adin sati biyu su kawo duk mutumin da ake kira da sunan tsaro in ba shi (shugaban kasar) da jami'an tsaro ba.
"Ni na san kwarewar jami'an tsaron Najeriya, a kayan aiki da kwarewa, wallahi za su kamo kowanene."
2. Kamo wadanda ke rike bindiga da masu ba da umarni
Sheikh Daurawa ya ci gaba da cewa jami'an tsaron Najeriya za su yi aiki ne kawai idan aka ba su umarni, don haka akwai buƙatar shugaban kasa ya dauki mataki.
"Shugaban kasa ya fada wa jami'an tsaro cewa, akwai wadanda ke rike bindiga kuma suna ba da umarni a harkar tsaro, a kamo su a raye ko a mace a cikin sati biyu.
"Idan kuma ba za ku iya ba, to ku ajiye inifom dinku, ku ga abin da zai faru."
Tashin hankalin da manoma suke fuskanta a Arewa
Game da hare-haren da ake kai wa manoma a jihohin Arewa, Daurawa ya ce:
"Akwai manoman da suka je gona, aka fille kawunan su a Maiduguri, laifin sa kawai don sun shiga gona su yi noma."
Legit ta ruwaito cewa wannan lamarin ya faru ne a kauyen Rann, wanda ke iyaka da jihar Borno a ranar Litinin 23 ga watan Mayun 2022.
Daurawa ya yi murabus daga shugaban Hisbah na Kano?
A 'yan kwanakin da suka gabata, jita-jitar cewa Sheikh Aminu Daudawa ya yi murabus daga shugaban hukumar Hisbah ta Kano ya cika kafofin sada zumunta.
Legit Hausa ta tuntubi hukumar Hisbah inda ta samu tabbacin cewa labarin ƙanzon kurege ne kawai ake yadawa, malamin har yanzu shi ne shugaban hukumar.
Tun da fari dai, masu jita-jitar na cewa Daurawa ya yi murabus ne bayan da aka fitar da yarinyar nan ƴar TikTok, Murja Ibrahim Kunya daga gidan gyaran hali.
Asali: Legit.ng