Tsadar Rayuwa: APC, PDP da LP Sun Yi Martani Kan Zanga-Zangar da NLC Ke Yi a Fadin Najeriya

Tsadar Rayuwa: APC, PDP da LP Sun Yi Martani Kan Zanga-Zangar da NLC Ke Yi a Fadin Najeriya

  • Haƙiƙanin abin da ke faruwa a ƙasa shi ne tsadar rayuwa da kuma taɓarɓarewar tattalin arziƙi da manufofin Shugaba Tinubu ke haifarwa
  • Sai dai ƙungiyar ta NLC ta dage cewa abin da ya fi dacewa shi ne yin zanga-zanga domin nuna irin wahalhalun da ake fama da su
  • A safiyar ranar Talata ne jam’iyyun PDP da jam’iyyar Labour suka bayyana goyon baya ga ƙungiyar NLC a yayin da zanga-zangar ke yaɗuwa a faɗin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Manyan jam’iyyun adawa biyu, PDP da Labour Party (LP), sun goyi bayan zanga-zangar kwanaki biyu da ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta fara.

APC ta nuna adawa kan zanga-zangar NLC
Kungiyar kwadago na son Tinubu ya tsamo 'yan Najeriya daga halin kunci Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

APC ta yi fatali da zanga-zangar NLC

Hakan dai ya faru ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ta nuna damuwarta kan cewa za a iya gurɓata zanga-zangar ta NLC.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: NLC ta samu gagarumar matsala kan zanga-zanga, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata tattaunawa ta daban da suka yi da jaridar The Punch a Abuja, jam’iyyun adawar sun bayyana cewa matsalar tattalin arziƙi ta isa ta sa talakawa su haɗa kai domin nuna adawa da gwamnatin tarayya.

A safiyar Talata, 27 ga watan Fabrairu, ƙungiyar ta fara zanga-zangar a faɗin Najeriya.

Zanga-zangar na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan gwamnatin tarayya da NLC sun kasa cimma matsaya.

PDP, LP sun bayyana goyon bayansu ga zanga-zangar NLC

Da yake magana da jaridar The Punch, mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP na ƙasa, Abdullahi Ibrahim, ya ce jama’a a shirye suke a kodayaushe su bijirewa duk wata manufa ta ƙyamar mutane.

Ibrahim yace:

"Don haka NLC ta yi abin da ya dace. PDP ta yarda da matsayar ƙungiyar ƙwadago. Abin da ke faruwa ya wuce hankalin ɗan Adam. Ba zai yiwu a yi tsammanin ƴan Najeriya za su naɗe hannayensu ba saboda gwamnatin APC ce ke mulki.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Jigon PDP ya fayyace gaskiya kan yiwuwar yin hadaka

"Ƙungiyar NLC ta mamaye tituna lokacin PDP. Haka suka yi a lokacin mulkin soja. Ban ga dalilin da zai sa wani ya yi tunanin ƙungiyar NLC ba za ta kawo cikas ga wannan gwamnati ba.
"Mutane ba su taɓa kasancewa a yanayi mafi muni ba kamar yadda muke gani a yau. Ƙarfin sayen abubuwa a ƙasar nan ya ragu. Haka kuma hauhawar farashin kayayyaki ya yi yawa. Ya kamata kowa ya fito don wannan zanga-zangar, ciki har da ma'aikata, ƙungiyoyin farar hula da ƴan kasuwa. PDP na goyon bayan wannan zanga-zangar."

Har ila yau, kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Yunusa Tanko, ya jaddada cewa, jama’a na da haƙƙin huce haushi kan wasu manufofin da za su cutar da su.

Jaridar Channels tv ta ruwaito cewa a jihar Akwa Ibom, kwamishinan ƴan sandan jihar, Waheed Ayilara, ya girke jami'an ƴan sanda 3,200 domin gudanar da zanga-zangar.

Kara karanta wannan

APC ta shiga matsala yayin da dan takarar gwamna ya yi barazanar daukar mataki 1 a kanta

Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Majalisar Tarayya

A wani labarin kuma, kun ji cewa masu zanga-zanga ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, sun dira a majalisar dokokin tarayya.

Masu zanga-zangar dai sun isa majalisar ne domin nuna ɓacin ransu kan yadda rayuwa ke cigaba da tsada a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel