Tsadar Rayuwa: NLC Ta Samu Gagarumar Matsala Kan Zanga-Zanga, Bayanai Sun Fito

Tsadar Rayuwa: NLC Ta Samu Gagarumar Matsala Kan Zanga-Zanga, Bayanai Sun Fito

  • Ƙungiyar ƙwadago ta NLC na shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairun 2024
  • Wasu ƙungiyoyin fararen hula sun nuna rashin amincewa da NLC kan zanga-zangar da da ta shirya yi a faɗin ƙasar nan
  • Ƙungiyoyin guda 65 sun yi gargaɗin cewa yajin aikin da zanga-zangar na iya haifar da rikici da kuma janyo wa ƴan Najeriya wahala

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyoyin fararen hula 65 (CSO) sun fice daga zanga-zangar da ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta shirya gudanarwa.

Kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito, ƙungiyoyin sun fice ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, saboda tsoron kada ɓata gari su shigo zanga-zangar.

Kara karanta wannan

APC ta shiga matsala yayin da dan takarar gwamna ya yi barazanar daukar mataki 1 a kanta

Kungiyoyi sun fasa shiga zanga-zangar NLC
NLC ta samu matsala kan zanga-zanga Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

A cewarsu, idan ƴan daba suka shigo zanga-zangar ta NLC, hakan na iya ƙara tsananta wahalhalun da ake fuskanta a ƙasar nan, rahoton Vanguard ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangane da yuwuwar kawo cikas a zanga-zangar, ƙungiyoyin a ƙarkashin gamayyar 'Coalition of Civil Society Organisations Forum' sun ce ba za su shiga zanga-zangar ba.

Meyasa ƙungiyoyin suka fasa shiga zanga-zangar?

Gamayyar ƙungiyoyin a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da kodinetanta, Buba Mohammed da sakatarenta, George Phillips suka fitar, sun bayyana cewa suna yin "namijin ƙoƙari" na ganawa da gwamnati don warware matsalolin cikin ruwan sanyi.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Duk wani yunƙuri na shiga yajin aikin gama gari a cikin wannan mawuyacin lokaci na yunwa da taɓarɓarewar tattalin arziƙi, ƴan daba da suke jiran ƴar ƙaramar dama domin tafka ta'asa a wuraren kasuwanci da kasuwanni, ka iya shigo wa a ciki su kawo cikas."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Babban malamin addini ya tura sako mai muhimmanci ga Shugaba Tinubu

NLC ta tsayar da ranakun Talata 27 ga watan Fabrairu da kuma Laraba 28 ga watan Fabrairu domin gudanar da zanga-zangar.

'Ba Ja Da Baya Kan Zanga-Zanga' - NLC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyana cewa ba gudu ba ja da bayan kan zanga-zangar da ta shirya.

Shugabannin ƙungiyar ta NLC sun ce wannan aiki da suke shiryawa bai saba doka ba, kuma ba su nufin kawo tashin hankali da tarzoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel