'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Al'umma a Wani Sabon Hari

'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Al'umma a Wani Sabon Hari

  • An shiga jimami a ƙauyen Umuoji na ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra bayan harin da ƴan bindiga suka kai a ƙauyen
  • Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai ƙauyen, sun halaka shugaban ƙauyen bayan sun dira har cikin gidansa
  • Kakakim rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ƴan sanda na ci gaba da gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Wasu ƴan bindiga da har yanzu ba a san ko su waye ba sun kashe shugaban al’umma a ƙauyen Umuoji a ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra, Silas Onyima.

Ko da yake, har yanzu babu cikakkun bayanai kan abin da ya faru, an tattaro cewa ƴan ta’addan wadanda yawansu ya kai 15, sun kai farmaki gidan marigayin a yammacin ranar Juma’a inda suka harbe shi har lahira wanda hakan ya jefa al’umma cikin firgici.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Babban malamin addini ya tura sako mai muhimmanci ga Shugaba Tinubu

'Yan bindiga sun kai hari a Anambra
'Yan bindiga sun tafka ta'asa a jihar Anambra Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

TABLE OF CONTENTS

Wata majiya ta shaida wa jaridar The Punch cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Marigayin shi ne sabon shugaban ƙauyenmu, kuma ya taɓa gudanar da wani zaɓe a ƙauyen. An kashe shi a ranar Juma'a da yamma lokacin da wasu miyagu suka dira a gidansa suka harbe shi har lahira."

Me.hukumomi suka ce kan lamarin?

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, ya ce an baza jami’an ƴan sanda a yankin.

A kalamansa:

"Yan sanda suna sane da wannan lamarin. Mun samu labarin kuma mun tura jami'anmu zuwa yankin. Jami'anmu sun je wajen bayan da muka samu bayanin, sai suka tarar da mutumin ƙwance cikin jini.
"An gano gawar mamacin kuma an ajiye shi a dakin ajiyar gawa tare da taimakon wasu ƴan uwansa. Har ila yau, muna aiki tare da wasu shaidun gani da ido da kuma mutanen ƙauyen don taimakawa wajen gano waɗanda suka aikata laifin, kuma ana ci gaba da bincike.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kwantan ɓauna, sun kashe babban ɗan sanda yana tsaka da aiki a jihar PDP

Ƴan Bindiga Sun Halaka Jami'in NDLEA

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka wani jami'in hukumar NDLEA a jihar Sokoto.

Ƴan bindigan waɗanda suka tare hanya, sun kuma yi awon gaba da wasu mutum.uku zuwa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel