"A Shigo da abinci" TUC Ta Gano Hanaya 1 da Zata Share Hawayen Talakawa, Ta Aike da Saƙo Ga Tinubu

"A Shigo da abinci" TUC Ta Gano Hanaya 1 da Zata Share Hawayen Talakawa, Ta Aike da Saƙo Ga Tinubu

  • Ƙungiyar kwadago TUC ta ƙasa ta bayyana abinda take ganin shi ne mafita a Najeriya yayin da ake fama da tsadar kayan abinci
  • Yayin hira da ƴan jarida, shugaban TUC na ƙasa, Festus Osifo, ya bukaci Bola Tinubu ya bada damar shigo da abinci daga ƙasashen waje
  • A cewarsa, hakan zai taimaka wajen daƙile hauhawar kayan abincin da mutane ke kuka da shi a halin yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƙungiyar kwadago Trade Union Congress of Nigeria (TUC) ta bai wa gwamnatin tarayya shawarar hanyar da zata magance ƙarancin abinci cikin mako biyu.

Kamar yadda Punch ta tattaro, TUC ta buƙaci gwamnatin tarayya ta fara shigo da kayayyakin abinci domin rage hauhawar farashin kayansu a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rantsar da kwamishinan NPC, ya shiga muhimmin taro da jiga-jigai a Villa

Shugaban TUC da Bola Tinubu.
Tsadar Rayuwa: "A fara shigo da abinci" TUC ta aike da sako ga Shugaba Tinubu Hoto: Festus Osifo, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban TUC, Festus Osifo ne ya bayyana haka a taron manema labarai kan matsin tattalin arzikin da kasar nan ke ciki ranar Litinin a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, ‘yan Najeriya ba su taba shiga irin wannan wahalhalun na tsadar rayuwa ba ko a lokacin mulkin soja.

Ya ƙara da cewa waɗannan matsalolin sun samo asali ne daga rashin maida hankalin gwamnati wajen samar da kaya a cikin gida da kuma ba su fifiko.

Ina mafita kan halin da ake ciki?

Shugaban TUC ya ce:

"Ƴan Najeriya na buƙatar su ji su a ƙoshe ta yadda zasu iya fahimtar kyaun tsarukan da gwamnati ta ɓullo da su. Ya kamata a sassauta kokarim wadatar abinci a cikin gida.
"Ya kamata gwamnatoci na kowane mataki su gaggauta zuwa su siyo isassun kayan abinci daga sassa daban-daban na duniya tare da raba wa ga ƴan Najeriya marasa galihu.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

"Shigo da abinci daga waje a wannan lokaci zai taimaka wajen rage hauhawar farashinsu a kasa. Ya kamata FG ta bada izinin shigo da abincin da yan Najeriya zasu ci nan da makonni biyu masu zuwa."

Osifo ya shawarci shugaban Ƙasa, Bola Tinubu da ya gaggauta karfafa tawagar da ke tafiyar da tattalin arzikin ƙasar nan a gwamnatinsa, Channels tv ta ruwaito.

Zanga-zanga ta ɓalle a jihohi 2

A wani rahoton kuma Fararen hula sun bazama kan tituna zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihohin Edo da Osun ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2024.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan zanga-zangar da aka yi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo duk kan halin da mutane suka shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel