Yanzu: A Karshe, Kalu Ya Zama Mataimakin Kakakin Majalisa Ta 10, Bayan Kai Ruwa Rana

Yanzu: A Karshe, Kalu Ya Zama Mataimakin Kakakin Majalisa Ta 10, Bayan Kai Ruwa Rana

  • Honarabul Benjamin Kalu ya yi nasarar zama mataimakin kakakin majalisar wakilai a majalisar Tarayya ta 10
  • Benjamin ya gaji kujerar tsohon matamakin kakakin majalisar ne Idris Wase a zaben da aka gudanar a yau Talata
  • An rantsar da shi da misalin karfe 12:21 na rana a harabar majalisar a yau Talata 13 ga watan Yuni a Abuja

FCT, Abuja - Dan majalisa mai wakiltar mazabar Bende ta Tarayya a jihar Abia, Benjamin Kalu ya zama mataimakin kakakin majalisar wakilai ta Tarayya.

Kalu shi ne wanda jam'iyyar APC ta zaba a baya don gadar kujerar mataimakin majalisar ta 10.

Benjamin Kalu ya zama mataimakin kakakin majalisar wakilai
Dan Majalisa Benjamin Kalu Daga Jihar Abia. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

An rantsar da shi da misalin karfe 12:21 a ranar Talata 13 ga watan Yuni a majalisar, cewar gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Burin ’Yan Kwankwasiya Ya Cika, Dan NNPP Ya Zama Shugaban Majalisa a Kano

Benjamin Kalu ya gaji kujerar mataimakin majalisar, Wase

Benjamin Kalu ya gaji kujerar mataimakon majalisar ne daga tsohon mataimakin kujerar majalisar a wurin Honarabul Idris Wase.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da Abbas Tajudden daga jihar Kaduna ya kasance kakakin majalisar ta 10 bayan doke Idris Wase da Aminu Jaji a ranar Talata 13 ga watan Yuni.

Abbas ya samu kuri'u 352 a cikin 359 yayin da Jaji da Wase suka samu kuri'u uku ko wanne, cewar Premium Times.

Yawan mambobin da ko wace jam'iyya ta ke da shi

Jam'iyyar APC mai mulki ta na da mambobi 170 daga cikin 360 na majalisar, yayin da jam'iyyar PDP ke da mambobi 100, jam'iyyar Labour kuma mambobi 35 sai NNPP mai mambobi 20.

'Yan majalisu da dama sun nuna sha'awarsu ta tsayawa takarar majalisar ta 10 wanda suka hada da Wase da Jaji da Alhassan Ado Doguwa da kuma Yusuf Gagdi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tajudeen Abass Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai

Sauran sun hada da Aliyu Betara da Abdulrahman Olawuyi da Princess Onuoha da sauransu, yayin da dukkan masu sha'awar takarar suka janye wa Abbas.

Sai dai Wase da Jaji sun tsaya kekam sun ki janyewa daga takarar ta su.

Tajudeen Abass Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai Ta 10

A wani labarin, Honarabul Tajudden Abbas ya yi nasarar zama kakakin majalisar wakilai ta 10.

Tajudden wanda jam'iyyar APC ta zaba a matsayin wanda zai gaji kujerar ta jawo cece-kuce a tsakanin mambobin majalisar.

Abbas ya samu kuri'u 352 daga cikin 359 na mambobin majalisar, yayin da Wase da Jaji suka samu uku ko wannensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.