‘Yan Canji Sun Fara Gujewa Dalar Amurka a Sakamakon Karyewar da take yi a kasuwa

‘Yan Canji Sun Fara Gujewa Dalar Amurka a Sakamakon Karyewar da take yi a kasuwa

  • ‘Yan canjin kudi a jihar Adamawa sun fara tsoron taba Dalar Amurka, ganin yadda farashi ke yawo
  • Masu harkar BDC sun tanadi tulin Daloli domin su ci riba, sai kurum darajar kudin wajen ya fara sauka
  • A dalilin sauyin farashin da aka samu a baya-bayan nan, ‘yan kasuwa sun gamu da asara mai yawa

Adamawa - Masu harkar canjin kudi a jihar Adamawa sun soma watsi da karbe kudin kasashen ketare saboda yadda kasuwa ta birkece a halin yanzu.

Daily Trust ta kawo rahoto a karshen makon jiya da ya nuna cewa faduwar Dalar Amurka a kasuwar canji ya jawowa kudin kasashen waje bakin jini.

‘Yan canji sun koma kin karbar Dala da sauran takwarorinta daga hannun mutane domin sus aida saboda rashin tabbas, ganin yadda darajarsu take fadi.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Bindige Dan Sa-kai Da Wasu Mutane 4 a Wata Jahar Arewa

Wasu ‘yan canji da aka yi hira da su a wata kasuwa a Jimeta da ke garin Yola sun shaidawa jaridar cewa karyewar Dala a kasuwa ya birkita masu lissafi.

Dala ta koma yin kasa a kasuwa

A yayin da farashin Dala daya ta kai N910 kwanakin baya, yanzu ana maganar ba ta kai N700 ba. Yadda darajar yake sauka yana tada hankalin ‘yan canji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton Nairaland ya nuna ‘yan kasuwa sun tafka asara a dalilin saukar farashin Dala.

Daloli
Dalolin Amurka Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Mun rasa N200 a kan duk $1

Shugaban kungiyar BDC watau ‘yan canji na reshen jihar Adamawa, Lawan Mai Yasin, ya bayyana cewa sun yi asara bayan sayen kowace $1 a kan N870.

Jim kadan bayan ‘yan canji sun saye Dalar a kan wannan farashi, sai ta karye zuwa N680 a kasuwar canji. Wannan ya sa aka rasa kusan N200 a kan duk $1.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

Lawan Mai Yasin yace abokan aikinsa sun daina sayen kudin kasar wajen a halin yanzu, za su zura idanu su lura da yadda kasuwar ke tafiya domin gudun asara.

Kamar yadda Mai Yasin ya shaida, ana fama da rashin tabbas a yau, ‘yan kasuwa sun kashe kudi wajen mallakar Dala, kafin a je ko ina sai farashin ya ruguzo.

A dalilin wannan ‘yan kasuwa da-dama sun daina sayen Dalar Amurkar a yanzu. Wata majiya tace idan kuwa za a saya Dalar, sai ayi wa mutum tayin banza.

Naira ta zaburo daga baya

Kun ji labari Dala ta tashi sosai a bayan Gwamnan CBN ya bada sanarwar za a canza manyan takardun kudi, daga baya kuma sai lissafin ya fara canzawa.

A makonnin da ya gabata sai da masu Dalar Amurka suka saidawa jama’a $1 a kan N910. Yanzu kuwa nema ake yi farashin ya tsaya a kan N7000 a kasuwa.

Kara karanta wannan

‘Dan Takarar Gwamnan PDP na Borno Ya Fallasa Yadda Harin da Aka Kaiwa Tawagar Atiku Ya Faru

Asali: Legit.ng

Online view pixel