Murna Yayin da Aka Fadi Lokacin Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Jihar Arewa

Murna Yayin da Aka Fadi Lokacin Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Jihar Arewa

  • Kwamishinan ƴan sandan jihar Zamfara ya bayyana cewa an tanadi dukkanin kayan aikin da ake buƙata domin kawo ƙarshen masu tada ƙayar baya a jihar
  • CP Kolo Yusuf ya ce nan da wata uku masu zuwa da yardar Allah matsalar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane za ta zo ƙarshe
  • Jihar Zamfara dai ta daɗe tana fama da matsalar rashin tsaro wacce ta salwantar da rayukan mutane masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Kwamishinan ƴan sandan jihar Zamfara, CP Kolo Yusuf ya bayar da tabbacin cewa ana aiki tuƙuru domin kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga da garkuwa da mutane a jihar.

Jaridar Channels tv ta kawo rahoto cewa kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da ta jiha sun tanadi dukkanin abubuwan da ake buƙata domin ganin an kawo ƙarshen matsalar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kwantan ɓauna, sun kashe babban ɗan sanda yana tsaka da aiki a jihar PDP

CP Kolo ya fadi lokacin kawo karshen 'yan bindiga a Zamfara
CP Kolo ya ce nan da wata uku 'yan bindiga za su zama tarihi a Zamfara Hoto: @ZamfaraPoliceNg
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne dai yayin da yake jawabi ga ƙungiyoyin kwadago na jihar da shugabannin addinai da ƙungiyoyin farar hula da kuma ƴan jarida a ranar Alhamis kan buƙatar kawar da shirin yajin aikin da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan, cewar TVC News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me kwamishinan ya ce kan tsaro a Zamfara?

A kalamansa:

"Wannan matsalar ba yau ta fara ba. Kuma gwamnati mai ci ta duƙufa wajen magance matsalar. Babbar matsalar da ke tattare da hakan ita ce janye tallafin man fetur, kuma ba wannan gwamnati ta yi ba.
"Don haka ya kamata mu yi hakuri da wannan gwamnati domin ba wannan gwamnatin ce ta janye tallafin man fetur ba. Abin da wannan gwamnati ke buƙata a yanzu shi ne addu’a.
"Mutane nan da can suna kira da a shiga yajin aiki. Hatta ƴan kwadagon sun so shiga yaji aiki, amma sun saurare ni bayan na roƙe su, inda suka dakatar da barazanarsu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki kan bayin Allah, sun kashe mutane tare da tafka ta'asa mai ban tausayi

"A lokacin da dukkan ku da ke wajen nan kuka daina aiki, za ku durƙusar da jihar nan. Ga ƴan bindiga suna nan sun hana mutane su yi noma. Yanzu barci ya ƙaurace min.
"Ina ci gaba da kiran DPOs da kwamandojin yanki don magance matsalar. Kuma da yardar Allah nan da wata uku masu zuwa za a magance dukkan matsalolin.
"Gwamnatin tarayya da ta jiha sun samar da dukkan abubuwan da ake buƙata don kawo ƙarshen masu tada ƙayar bayan. Don haka mu marawa gwamnati baya don kawo karshen tada ƙayar baya, mu manta da shiga yajin aiki."

Gwamnatin Zamfara Ta Hana Sayar da Biredi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki matakin hana sayar da biredi da man fetur a jarkoki ga masu ababen hawa a jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne bayan ta gano wasu ɓata gari na yi wa ƴan bindiga safarar kayayyakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel