“Ban San Me Ya Hau Kaina Ba”: Matashi Ya Sheke Mahaifiyarsa, Ya Kona Gidansu

“Ban San Me Ya Hau Kaina Ba”: Matashi Ya Sheke Mahaifiyarsa, Ya Kona Gidansu

  • Rundunar 'yan sandan jihar Cross River ta kama Idara Aniefiok, matashi 'dan shekaru 29 da ya kashe mahaifiyarsa
  • Marigayiya Ekaette Aniefiok Amos, mai shekaru 62, ta yi nasarar fita daga gidansu bayan matashin ya cinna masa wuta, da nufin babbaka ta a ciki
  • Sai dai kuma, yaron ya sake bin dattijuwar inda ya sheme ta da gatarin karfe a kai, ta kuma mutu a hanyar zuwa asibiti

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Calabar, Cross River - Wani matashi 'dan shekaru 29 mai suna Idara Aniefiok Amos, wanda ake zargi da yi wa mahaifiyarsa, Ekaette Aniefiok Amos, kisan gilla ya nuna shiga rudani kan abin da ya aikata, yana mai cewa bai san dalilinsa na yin hakan ba.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2, dan gwagwarmayar kafa ƙasar Yarbawa Igboho ya dawo Najeriya, an gano dalili

Rundunar 'yan sandan jihar Cross River ta gurfanar da Idara cikin mutane 15 da aka kama kan aikata laifuka daban-daban, a ranar Juma'a, 23 ga watan Fabrairu.

An kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa
“Ban San Me Ya Hau Kaina Ba”: Matashi Ya Sheke Mahaifiyarsa, Ya Kona Gidansu Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Gyogon Grimah, ya bayyana a yayin gurfanar da su a garin Calabar, cewa Idara ya zargi mahaifiyarsa da hannu a tabarbarewar dukiyarsa kafin ya kashe ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma cinna wa gidansu mai lamba 22 a unguwar Asuquo Asuquo, Calabar ta Kudu wuta.

Rundunar 'yan sanda ta tuna yadda Idara ya kashe mahaifiyarsa

Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana cewa mahaifiyar Idara ta yi nasarar fita daga gidansu bayan wanda ake zargin ya cinna masa wuta.

Ya ce wanda ake zargin ya sake kama ta, sannan ya yi amfani da gatarin karfe wajen bugunta a kai, inda ta mutu a hanyar zuwa asibiti.

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

Jaridar The Nation ta nakalto kwamishinan 'yan sandan yana cewa:

"Mahaifiyar, Ekaette Aniefiok Amos mai shekaru 62 ta tsallake rijiya da baya daga gobarar da ta taso a gidan amma sai wanda ake zargin ya yi amfani da gatarin karfe wajen bugun mahaifiyarsa a kai. Matar ta mutu a hanyar zuwa asibiti."

Jaridar Blueprint ta rahoto cewa yayin hira da shi, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa wani abu ne ya shiga jikinsa sannan ya kai shi ga aikata hakan, ya ce:

"Maganar gaskiya ba zan iya yin bayanin abin da ya haddasa mani yin haka ba. A 'yan watanni da suka wuce, rayuwata ta tabarbare, amma ba zan iya bayanin komai ba yanzu."

Igboho ya zargi Buhari da yunkurin kashe shi

A wani labari na daban, mun ji cewa 'dan gwagwarmayar kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho, ya yi zargin cewa tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura jami'an DSS domin su kashe shi.

Igboho ya bayyana a ranar Juma'a, 23 ga watan Fabrairu, cewa ya dawo Najeriya ne yana mai imani da samun kariyar Ubangiji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel