Hazikin Matashi Ya Kera Otal da Katafaren Gida Daga Kwalaye, Basirarsa Ta Burge Mutane

Hazikin Matashi Ya Kera Otal da Katafaren Gida Daga Kwalaye, Basirarsa Ta Burge Mutane

  • Wani matashi da Allah ya yi wa baiwa a Instagram, Met Maquette, ya baje kolin fikirarsa na wani katafaren gida da otal da ya kera ta hanyar amfani da kwalaye
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu, Met ya baje kolin kyawawan gine-ginen na ban mamaki da ya kwaikwaya masu burgewa
  • Kamar dai kullun, jama'a da suka san kyawawan abubuwa sun garzaya sashinsa na sharhi domin bayyana ra'ayoyinsu tare da karfafa masa gwiwa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani hazikin matashi mai suna Met Mawuette a Instagram ya nunawa duniya baiwar da Allah ya yi masa ta hanyar kera otal da wani katafaren gida da kwalaye.

Ya kera gine-ginen da yake sha'awa a wurare daban-daban, mutum na iya ganin inda ya baje kolin katafaren otal din.

Kara karanta wannan

"Ba ta siyarwa bace": Uba ya mayarwa ango da kudin sadakin diyarsa, ya yi magana 1 mai ratsa zuciya

Matashi ya yi kere-kere da kwalaye
Hazikin Matashi Ya Kera Otal da Katafaren Gida Daga Kwalaye, Basirarsa Ta Burge Mutane Hoto: met_maquette_lofficiel.
Asali: UGC

Shafin Met Maquette na Instagram na kawo nishadi mara yankewa duba ga yadda matashin ke baje fikirar da Allah ya yi masa a soshiyal midiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake yi wa daya daga cikin bidiyoyinsa take, matashin ya sa "samfurin Villa da aka yi da kwali."

"Tsarin otal da aka yi da kwali," taken da ya yi wa bidiyon da ke nuna tsarin wani hadaden otal.

Kalli bidiyoyin a kasa:

Jama'a sun yi martani kan hazikancin matashin

Madusu_fashion_abaya_model ta yi martani:

"Sannu da kokari, 'dan uwa abin sona ❤️❤️.

Obiba_adepa yace:

"Babban aiki, 'dan uwa."

OdisaMayo ya yi martani:

"Allah ya yi maka baiwa. Ka ci gaba a haka."

GikpaLowi ya rubuta:

"Na so wannan. Wooooooow."

JazzyChacha ya ce:

"Wow. Allah ya albarkace ka da baiwa. Ka gode masa a kullun."

Kara karanta wannan

"Tsoho ya dawo": Karamin yaro ya fashe da dariyar jin dadi yayin da ake yi masa susan kunne

Yvedacadet ya yi martani:

"Wowwwwww."

Cassialuciana93 ta yi martani:

"Ya yi kyau ina taya ka murnba."

Matasa sun yi gini babu siminti

A wani labarin, mun ji cewa masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga wani bidiyo na wasu matasa biyu da ke gina gida ba tare da amfani da siminti ba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tsadar siminti a fadin kasar wanda ya jefa 'yan Najeriya cikin wani yanayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel