EFCC: Kotu Ta Karbe Naira Biliyan 1.5 Daga Hannun Tsohon Shugaban Hukumar NIRSAL

EFCC: Kotu Ta Karbe Naira Biliyan 1.5 Daga Hannun Tsohon Shugaban Hukumar NIRSAL

  • EFCC ta fara samun nasara a kan Aliyu Abatti Abdulhameed a shari’ar da ta ke yi da tsohon shugaban na hukumar NIRSAL a kotu a Abuja
  • Alkalin ya bada umarnin wucin-gadi na karbe N1.58bn da aka samu bayan gurfanar da Steve Olusegun Ogidan da kamfanoninsu
  • Tun ranar 5 ga Fabrairun 2024 aka bada zartar da wannan hukunci, kotun tarayyar za ta iya maidawa Najeriya kudin din-din-din

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Wata babbar kotun tarayya mai zama a garin Abuja, ta bada umarni a soma karbe N1.5bn daga hannun Aliyu Abatti Abdulhameed.

Alkali Inyang Ekwo ya bada wannan umarni a cewar Daily Trust da EFCC ta shigar da karar tsohon shugaban hukumar NIRSAL a kotu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi sabon nadi mai muhimmanci a hukumar ‘Immigration’ ta Najeriya

EFCC - Nirsal
EFCC na binciken tsohon shugaban NIRSAL Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Aliyu Abatti Abdulhameed a NIRSAL

Aliyu Abatti Abdulhameed ya rike kujerar shugaban hukumar NIRSAL mai bada aron kudin noma a lokacin Muhammadu Buhari yana mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hukuncin da ya soma gabatarwa, Mai shari’a Inyang Ekwo ya bukaci a wallafa umarnin da ya bada a manyan gidajen jaridun kasar nan.

Manufar yin hakan shi ne duk wanda yake da sha’awar dukiyar da aka karbe, sai ya garzaya kotun tarayyar cikin kwanaki 14 ya yi magana.

NIRSAL v EFCC: Lokacin da aka bada ya cika

Aminiya ta ce tun ranar 5 ga watan Fubrairun nan Inyang Ekwo ya zartar da hukuncin nan.

Alkali ya bada tsawon makonni biyu domin bada dama ga wanda zai kalubalanci karbe kudin, a maida cikin asusun gwamnatin tarayya.

Lauyoyin hukumar EFCC sun maka Aliyu Abatti Abdulhameed, Dr. Steve Olusegun Ogidan da wasu abokan aikinsu da kamfanoninsu a kotu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya samu babbar nasara a babbar kotun jihar Kano kan matsala 1 da aka jefa shi

Ana zargin wadannan mutane da mukarrabansu da kamfanoninsu da wawurar biliyoyi. Dama tun tuni aka ji labari an fara yin bincike.

G.I. Ndeh Esq wanda ya tsayawa EFCC ya nemi kotu ta rike N1,582,000 da ake zargin an samu a wajen binciken hukumar bada rancen kudin.

Kotun da ke Abuja ta amince da bukatun hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya. A ranar 20 ga watan Maris za a cigaba da yin shari’ar.

Ana binciken Aliyu Abdulhameed a NIRSAL

Kwanaki an ji labari ana tuhumar tsohon jami’in watau Aliyu Abdulhameed da satar N5.2bn na tsarin noman alkalama aka shiryawa manoma.

Sannan ana zargin Aliyu Abdulhameed ya tsere da motocin ofis fiye da 30 da Shugaba Muhammadu Buhari ya kore shi daga aiki a 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel