Shugaba Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci a Hukumar ‘Immigration’ Ta Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci a Hukumar ‘Immigration’ Ta Najeriya

  • Shugaba Tinubu ya nada DCG Kemi Nanna Nandap a matsayin Kwanturola-Janar ta hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS)
  • DCG Nandap za ta karbi ragamar mulki daga hannun Wura-Ola Adepoju, wadda wa'adin aikinta ke karewa a ranar 29 ga Fabrairu, 2024
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin DCG Kemi Nanna Nandap a matsayin Kwanturola-Janar ta hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS).

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasar, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa , ya ce nadin zai fara aiki daga ranar 1 ga Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya samu babbar nasara a babbar kotun jihar Kano kan matsala 1 da aka jefa shi

Tinubu ya nada Nanna Nandap matsayin sabuwar shugabar hukumar 'immigration'.
Tinubu ya nada Nanna Nandap matsayin sabuwar shugabar hukumar 'immigration'.
Asali: Facebook

Dada Olusegun, mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan shafukan sada zumunta ne ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, nada DCG Nandap ya yi daidai da "sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ke yi a cikin ayyukan hukumar".

Ngelale ya ce:

“DCG Nandap za ta karbi ragamar hukumar daga hannun Misis Caroline Wura-Ola Adepoju, wacce wa’adinta zai kare a ranar 29 ga Fabrairu, 2024.
“Kafin nadin ta a matsayin Kwanturola-Janar, Nandap ta kasance mataimakiyar Kwanturola-Janar mai kula da bangaren hijira na hukumar."

Shugaban ya yi hasashen cewa sabuwar shugabar za ta karfafa gyare-gyaren da ake yi a hukumar tare da samar da ingantacciyar hanyar isar da aiki mai inganci ga ‘yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel