Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Kori Babban Managan Hukumar NIRSAL

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Kori Babban Managan Hukumar NIRSAL

  • Kimanin yan Nigeria Dubu 500 hukumar tace sun amfana da kashin farko na tallafin hukumar a shekarar data gabata
  • Aiyukan Hukumar sun kara bayyana ƙarara bayan da gwamnati ta fara taimakawa kananan manoma a fadin kasar
  • Hukumar NIRSAL dai hukumace da take bada tallafin kayan noma, wani lokacin kuma bashin kayan noma dan habaka shi
yanzu
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Kori Babban Managan Hukumar NIRSAL Hoto: legit
Asali: UGC

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban hukumar NIRSAL yau, Juma'a biyo bayan rahotan da Hukumar hana cin hanci da rashawa EFCC ta aike masa na samun babban manajan hukumar da almundaha da dukiyar kasa.

An cire Aliyu Abdulhameed ne dai bayan da wani rahoton da jaridar Daily Trsut ta fitar a watan January na wannan shekarar inda ya yuna manajan Hukumar na da hannu a wata cuwa-cuwa a hukumar.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Dai Aminu Zai Gana Da Shugaba Buhari A Villa Yau, Bayan Aisha Buhari Ta Janye Karar Data Shigar

Ya Batun Yake Ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A watan Janairun bana ne Jarida Daily Trust ta gudanar da bincike kan yadda NIRSAL ta karkatar da lamunce na bayar da lamunin rancen biliyoyin Naira na wasu kamfanoni masu zuba hannun jari don noman alkama na noman rani a Kano da kuma Jigawa.

Baya ga hukumar ta EFCC, ICPC da ‘yan sanda sun suma sun kaddamar da nasu binciken a kan lamarin.

Wasu majiyoyi na cikin gida da suka tabbatar da faruwar lamarin sun ce biyo bayan umarnin da fadar shugaban kasa ta bayar, an kori MD din ne da yammacin ranar Alhamis din da ta gabata, aka kuma fitar da shi daga harabar jim kadan bayan ya yi wa ma’aikatan jawabi a takaice.

Ko da yake har yanzu ba'a bayyana a hukumance ba, wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta ta ce Hukumar NIRSAL ta bukaci a nada mukaddashin MD.

Abdulhameed da mai magana da yawun NIRSAL, Anne Ihugba, ba su amsa kiran waya da sakonnin tes da da wakilin Daily Trust ya aika musu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel