Shettima Ya Fadi Babban Tanadin da Shugaba Tinubu Ya Yi Wa 'Yan Najeriya

Shettima Ya Fadi Babban Tanadin da Shugaba Tinubu Ya Yi Wa 'Yan Najeriya

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya kwantar da hankulan ƴan Najeriya yayin da ake ci gaba da fuskantar halin ƙunci a Najeriya
  • Shettima ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri domin akwai shirye-shirye masu kyau da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tanadar musu
  • Mataimakin shugaban ƙasan ya yi nuni da cewa maido da zaman lafiya a yankunan da ake fama da rashin tsaro na da muhimmanci ga shugaban ƙasan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa, Shugaba Bola Tinubu na da kyawawan tsare-tsare na inganta rayuwar al’umma.

Jaridar The Cable ta ce Shettima ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Asabar a garin Kafur na jihar Katsina lokacin da ya ƙaddamar da wani shirin tallafi da Ibrahim Masari babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin siyasa ya ɗauki nauyi.

Kara karanta wannan

Shugabannin majalisa za su gana da Shugaba Tinubu, bayanai sun fito

Shettima ya yi wa 'yan Najeriya albishir
Shettima ya ce Tinubu na da shirye masu kyau ga 'yan Najeriya Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi haƙuri da gwamnatin da Tinubu ke jagoranta, yana mai cewa shugabanci ya shafi nuna tausayi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane albishir Shettima ya yi ƴan Najeriya?

A kalamansa:

"Shugaban ƙasa ya yi matukar farin ciki da nuna goyon baya da tausayawa da Hon Ibrahim Kabiru Masari ya yi.
"Jagoranci ya shafi nuna tausayi da goyon baya ga jama'a. Shugaban ƙasa ya sanya al'ummar wannan ƙasa mai girma a zuciyarsa.
"Na zo nan ne domin in tabbatar wa mutanen Katsina da kuma yankin Arewa maso Yamma cewa akwai kyawawan tsare-tsare ga jama’a."

Mataimakin shugaban ƙasan ya kuma ƙara da cewa maido da zaman lafiya a yankunan da ake fama da matsalolin tsaro na da matuƙar muhimmanci ga Tinubu, rahoton jaridar Thisday ya tabbatar.

Shettima ya faɗi hanyar magance rashin tsaro a Najeriya

Kara karanta wannan

UAE ta cire takunkumin hana 'yan Najeriya biza? Fadar shugaban kasa ta fadi gaskiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan hanyar da za a bi domin magance matsalar rashin tsaron da ta addabi ƙasar nan.

Shettima ya yi nuni da cewa idan ana son a kawo ƙarshen matsalar dole ne sai an tsare iyakokin da ƙasar nan take da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel