Ma’aikata Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Wata Jihar Arewa, an Gano Dalili

Ma’aikata Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Wata Jihar Arewa, an Gano Dalili

  • Kungiyoyin kwadagon NLC da TUC na jihar Neja sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a wanda zai fara aiki daga yau Laraba
  • Wannan ya biyo bayan wasu matsaloli da kungiyoyin kwadagon suke ikirarin gwamnatin ta samu da ma'aikatan jihar
  • Shugabannin kungiyoyin sun ce ba za su janye daga yajin aikin ba har sai gwamnati ta cika wasu sharudda da suka gindaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Neja - Kungiyar kwadago a jihar Neja ta sanar da tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a jihar wanda zai fara aiki daga ranar Laraba 21 ga Fabrairu, 2024.

Kungiyar kwadagon ta ce ba za ta janye daga yajin aikin ba har sai gwamnati ta warware duk wasu sabani da ke tsakaninta da kungiyar kwadagon, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Bayan yunwa ta nakasa mutane, Gwamna a Arewa ya sake fitar da shinkafa don marasa karfi, an bi tsari

Ma’aikata a jihar Neja sun fara yajin aiki
Ma’aikata a jihar Neja sun gindayawa gwamnatin Neja sharuddan janye yajin aiki. Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

Shugabannin kungiyar NLC da TUC na jihar Idris A. Lafene da Ibrahim Gana ne suka bayyana hakan a wata wasika da suka aikewa ofishin sakataren gwamnatin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikata sun gindaya wa gwamnati sharudda

Kungiyar kwadagon ta bukaci gwamnatin jihar da ta sauya duk wasu nade-naden da ta yi na manyan daraktocin kudi, ayyuka da gudanarwa a hukumomin jihar.

Kungiyoyin sun bukaci gwamnati da ta sauya nadin shugabanni da mambobi da kwamishinonin dindindin na hukumar ma'aikatan kananan hukumomi.

Sauran bukatu sun hada da "gwamnati ta yi bayani karara a kan biyan albashin ma'aikata," kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar kwadagon, ta gargadi gwamnatin jihar kan nadin ma’aikatan da ba su cancanta ba a matsayin sakatarorin dindindin.

Sun kuma gargadi gwamnatin jihar da ta daina cin zarafin malamai da ‘yan bangaren ilimi kan cewar suna koya wa dalibai amfani da kalamai marasa kyau.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kano da sauran jihohi 3 da aka gudanar da mummunar zanga-zanga a Najeriya

Direbobin dakon fetur sun janye yajin aiki

A jiya Talata, Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyar direbobin NARTO sun janye daga yajin aikin da suka tsunduma a ranar Litinin bayan ganawa da gwamnati.

Tun da fari, direbobin sun shiga yajin aikin ne saboda matsalolin da suke fuskanta kama daga tsadar dizal da rashin kyawun hanya yayin dakon man fetur.

Gwamnatin tarayya ta sha alwashin duba matsalolin da direbobin suka ambata don samar da mafita mai dorewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel