Tinubu Ya Shiga Ganawar Gaggawa Da Tsohon Shugaban Kasa a Fadarsa, Bayanai Sun Fito

Tinubu Ya Shiga Ganawar Gaggawa Da Tsohon Shugaban Kasa a Fadarsa, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, Shugaba Tinubu na ganawa ta musamman da Janar Yakubu Gowon a Abuja
  • Tinubu na ganawar ce da tsohon shugaban kasar a mulkin soja a fadarsa da ke birnin Tarayya Abuja a yanzu haka
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan ita ce ganawarsu ta farko tun bayan hawan Shugaba Tinubu a watan Mayun 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu yanzu haka ya na ganawar sirri da tsohon shugaban kasa da ke birnin Tarayya Abuja.

Tinubu ya na ganawar ce da Janar Yakubu Gowon a fadarsa da ke birnin Tarayya Abuja, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasa ya fadi matakin da ya kamata 'yan Najeriya su 'dauka kan mulkin Tinubu

Tsohon shuga ban kasa ya shiga ganawar gaggawa da Tinubu a Abuja
Shugaba Tinubu ya shiga ganawar sirri da Janar Yakubu Gowon. Hoto: Yakubu Gowon, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Ganawa ta nawa Gowon ke yi da Tinubu a yau?

Wannan ita ce ganawarsu ta farko tun bayan hawan Shugaba Bola Tinubu kan karagar mulki a watan Mayun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gowon ya isa fadar shugaban kasar ce da misalin karfe 2:00 na yamma inda Tinubu ya tarbe shi.

Duk da ba a samu karin bayani kan dalilin ganawar ba, ana hasashen bai rasa nasaba da tattauna batun matsin tattalin arziki.

Shugaba Tinubu idan ba a manta ba ya cire tallafin mai a watan Mayun 2023 wanda shi ne musabbabin jefa 'yan kasar a wani hali.

Yaushe Gowon ya mullki Najeriya?

Tsadar rayuwar ta jawo zanga-zanga a wasu jihohin Najeriya inda suke neman kawo wa jama'a dauki.

Tsohon shugaban kasar ya shugabanci Najeriya a mulkin soja daga watan Agusta na shekarar 1966 zuwa watan Yulin shekarar 1975.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake korar wani da Buhari ya nada, ya sanar da wace zata maye gurbinsa

A mulkin Janar Gowon ne aka yi yakin basasa tsakanin sojojin Najeriya da kuma na yankin Biafra da ke neman 'yanci, cewar Leadership.

Majalisa ta daga yatsa ga Tinubu

A baya, mun baku labarin cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta fusata da kokarin kara kudin wutar lantarki da ake yi.

Majalisar ta ki amince da shirin cire tallafin wutar lantarkin yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali bayan cire tallafin man fetur.

Wannan na zuwa ne bayan Ministan Makamashi ya yi alkawarin cewa ba za su ci gaba da biyan kudaden tallafin wutar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.