Kano: Kungiya Ta Tura Muhimmin Sako Ga Majalisa Kan Mayar da Sunusi Kujerarsa, Ta Zayyana Dalilai

Kano: Kungiya Ta Tura Muhimmin Sako Ga Majalisa Kan Mayar da Sunusi Kujerarsa, Ta Zayyana Dalilai

  • Kungiyar “Yan Dangwalen Jihar Kano” ta tura wasika zuwa Majalisar jihar Kano kan sake duba masarautun jihar hudu
  • Kungiyar ta kuma bukaci bayan sake duba dokar a mayar da tsohon Sarki, Sunusi Lamido kan kujerarsa ta mulki
  • Kungiyar a cikin wata wasika da ta tura Majalisar a jiya Talata 5 ga watan Faburairu ta bukaci mayar tsohon Sarki Sunusi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Wata kungiya a jihar Kano ta rubuta wasika zuwa ga Majalisar jihar kan sake duba tsarin masarautun jihar.

Kungiyar mai suna “Yan Dangwalen jihar Kano” ta bukaci a sake duba dokar da ta kirkiri masarautun guda hudu.

Kungiya ta fara kira dawo da Sunusi Lamido kujerarsa a Kano
Kungiya 'Yan Dangwalen Kano" ta bukaci sake duba dokar masarautu a Kano. Hoto: Sunusi Lamido, Abba Kabir.
Asali: Original

Mene bukatar kungiyar a Kano?

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar da kotu ta tsige ya haye, APC ta doke PDP da kuri’u 600

Masarautun hudu sun hada da na Gaya da Rano da Karaye da Bichi wacce gwamnatin da ta shude ta kirkira, cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 5 ga wtan Disambar 2019 ce tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya kirkiri masarautun inda Majalisar ta amince da dokar nan take.

Watanni kadan da kirirar masarautun, Ganduje ya tube tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi, Media Talk Africa ta tattaro.

Kungiyar a cikin wata wasika da ta tura Majalisar a jiya Talata 5 ga watan Faburairu ta bukaci mayar tsohon Sarki Sunusi.

Wace shawara kungiyar ta bayar?

Sanarwar ta ce:

“Mun rubuta wannan takarda ga wannan ofishi mai daraja kan kirkirar masarutu hudu a Kano, muna son a sake duba dokar kan masarautun.
“Mun yi imanin cewa hada wadannan masarutu zai kara zaman lafiya da ci gaba ga al’ummar jihar.

Kara karanta wannan

'Za a gwabza': Mai tsare ragar tawagar Afrika ta Kudu ta shirya karawa da Super Eagles a gasar AFCON

“Muna rokon Majalisar da ta sake duba dokar da mayar da Sunus Lamido kan kujarsa ganin yadda hakan zai kara hadin kai a jihar da ma makwabta.”

Sanarwar ta kara da cewa Sunusi lokacin da yake kan karagar mulki ya tabbatar da himmatuwarsa wurin inganta zaman lafiya da hadin kai.

An fara kiran mayar da Sunusi kan mulki

Kun ji cewa tun bayan samun nasara a Kotun koli da Gwamna Abba Kabir ya yi aka fara kiraye-kirayen kujerar Sunusi Lamido.

Mutane da dama na neman a sake sabon Sarki kamar yadda aka samu sabon gwamna a jihar don samun daidaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel