Zanga-zanga Ta Barke a Kudancin Najeriya Kan Hukuncin Zaben Kano, Sun Tura Sako Ga Tinubu

Zanga-zanga Ta Barke a Kudancin Najeriya Kan Hukuncin Zaben Kano, Sun Tura Sako Ga Tinubu

  • Yayin da ake dakon hukuncin shari'ar zaben Kano, 'yan Arewa a Kudancin Najeriya sun yi zanga-zanga
  • Kungiyar 'yan Arewa da ke Kudancin kasar sun shawarci Tinubu da ya tabbatar an yi adalci yayin yanke hukuncin
  • Kungiyar ta kuma bukaci a bar wa Gwamna Abba Kabir kujerarshi don samar da zaman lafiya a jihar da ma Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - 'Yan Arewa mazauna Kudu maso Yammacin Najeriya sun yi zanga-zanga kan shari'ar zaben jihar Kano.

Kungiyar Arewa ta gudanar da zanga-zangar ce a birnin Ibadan da ke jihar Oyo inda ta ce ana son tuge wanda al'umma su ka zaba.

Masu zanga-zanga sun fito a Kudancin Najeriya kan hukuncin zaben Kano
Zanga-zanga a Kudanci kan hukuncin kotu a jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Mene ma su zanga-zangar ke cewa?

Kara karanta wannan

Wata sabuwa yayin da aka zargi Tinubu da haddasa rikicin siyasa a Kano

Mataimakin shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum reshen jihar, Shehu Idris ya koka kan halin da ake ciki a yankin Arewa, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabar mata a kungiyar, Aisha Isma'il ta ce yadda ake hukunta manyan 'yan siyasar yankin zai kara jefa ta cikin mawuyacin hali.

Kungiyar ta kirayi Shugaba Tinubu da ya saka baki wurin tabbatar adalci a shari'ar da ake yi, cewar Vanguard.

Ta kuma bukaci Tinubu da APC da kada su yi kokarin juya shari'ar zaben jihohi zuwa bangarensu.

Masu zanga-zangar sun yi kira na musamman kan shari'ar jihar Kano inda su ka bukaci a yi hukuncin adalci a Kano saboda duk abin da ya shafi jihar zai taba Arewacin Najeriya.

Wane shawara ma su zanga-zangar su ka bayar?

Shehu Idris ya ce:

"Ana son yin fashi da tsakar rana kan hukuncin kotu inda ake kokarin kawo cikas kan abin da mutane su ka zaba."

Kara karanta wannan

Kano: Ana son hukunta Abba ne don 2027, Masu zanga-zanga a Abuja sun fusata, sun ba da misali

Yayin da Aisha Isma'il ta bukaci Tinubu da ya ji bukatun mata kan yin adalci a shari'ar Kano.

Ta ce:

"Duk lokacin da giwaye ke fada, ciyawa ce ke shan wahala, mu na son a bar Abba Kabir a kan kujerarshi."

Kotu ta yi hukunci kan rusau a Kano

A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan rusau da Gwamna Abba Kabir ya yi a jihar.

Kotun ta rufe asusun bankunan jihar guda 24 wanda masu karar ke bukatar diyyar biliyan 30.

Asali: Legit.ng

Online view pixel