Tsadar Rayuwa: Bayan Kano da Minna, Sabuwar Zanga-Zanga Ta Barke a Wata Jihar Kudu

Tsadar Rayuwa: Bayan Kano da Minna, Sabuwar Zanga-Zanga Ta Barke a Wata Jihar Kudu

  • Zanga-zagar lumana ta barke a wasu sassa na jihar Oyo, inda maza da mata suka fito don nuna adawa kan tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya
  • Masu zanga-zagar suna dauke da kwalaye masu rubutu a jiki da ke yin kira ga gwamnati ta yi mai yiwuwa wajen kawo sauki a rayuwar talaka
  • An gudanar da zanga-zangar a wuraren da suka hada da unguwar Mokola, Sango da Iwo da ke cikin Ibadan, babban birnin jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ibadan, jihar Oyo - Zanga-zanga ta barke a jihar Oyo a ranar Litinin kan tsadar rayuwa, tsadar abinci da kuma tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun kai kazamin hari kan matafiya, sun tafka mummunar ɓarna a jihar Arewa

Zanga-zangar da aka fara ta daga unguwar Mokola da ke Ibadan, babban birnin jihar, an ga matasa rike da kwalaye da ke dauke da rubutuka na nuna bacin rai kan halin da kasar ke ciki.

Maza da mata sun gudanar da zanga-zangar luma kan tsadar rayuwa a jihar Oyo
Maza da mata sun gudanar da zanga-zangar luma kan tsadar rayuwa a jihar Oyo. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Wasu daga cikin kwalayen na dauke da rubuce-rubuce kamar su:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘A kawo karshen hauhawar farashin abinci’, ‘Talakawa na fama da yunwa’, ‘Tinubu, kar ka manta da alkawuran da ka dauka’, da dai sauransu, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Mazauna garin Mokola da ke jihar Oyo sun fito kan titi domin nuna adawa da rashin jin dadinsu kan tsadar rayuwa a kasar.

Sun rera wakoki daban-daban na yin kira ga gwamnatin tarayya da ta cika alkawuran zaben da ta yi, ta kuma kawo karshen wahalar da ake fama da ita a fadin Najeriya.

An kuma yi wata zanga-zangar Sango da Iwo

Kara karanta wannan

Jerin jihohin Najeriya 10 da aka fi samun kayan abinci da tsada, Kogi na kan gaba

An kuma gudanar da irin wannan zanga-zangar a yankin Sango da Iwo dake cikin Ibadan babban birnin jihar Oyo, kamar yadda

Masu zanga-zangar sun yi fatan gwamnati za ta yi la'akari da wadannan zanga-zangar ta kuma yi wani abu don rage radadin da talakawan Najeriya ke ciki.

An ga ‘yan sanda dauke da makamai a wurin zanga-zangar yayin da mutane ke nuna adawa da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki sakamakon cire tallafin man fetur.

Idan dai za a iya tunawa, a ‘yan makonnin da suka gabata an gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa da abinci a jahohin Neja, Filato, Kano, Sakkwato, da Osun da dai sauransu.

Zanga-zaga ta barke a jihar Neja kan tsadar rayuwa

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa zanga-zagar lumana ta barke a jihar Neja, don nuna adawa kan tsadar rayuwa a Najeriya.

An gudanar da zanga-zangar ne a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu, inda masu zanga-zagar suka mamaye manyan titunan Minna.

Amma dai rahotanni sun bayyana cewa rundunar 'yan sanda ta kama A'isha Jibrin, wacce ta jagoranci zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel