Haka Ba Zai Faru Ba, Majalisa Ta Yi Alkawari Kan Tsadar Mai da Wutar Lantarki Ga 'Yan Najeriya

Haka Ba Zai Faru Ba, Majalisa Ta Yi Alkawari Kan Tsadar Mai da Wutar Lantarki Ga 'Yan Najeriya

  • Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, Majalisar Dattawa ta nuna goyon bayanta ga 'yan kasar kan tsadar mai da wutar lantarki
  • Majalisar ta ce ta na yin duk mai yiyuwa don tabbatar da cewa ba a kara farashin man fetur da wutar lantarki ba
  • Wannan na zuwa ne bayan Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin wutar ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa a Najeriya ta ce ta na yin duk mai yiyuwa don tabbatar da cewa ba a kara farashin man fetur da wutar lantarki ba.

Kara karanta wannan

Ku bamu kwana 30, Masu sarrafa siminti sun gindaya sharuda ga Tinubu kan farashin, sun kawo mafita

Majalisar ta ce duk da karyewar darajar naira idan aka kwatanta da sauran kudaden duniya za ta dakile tashin farashin, cewar Arise TV.

Majalisa za ta tsayawa 'yan Najeriya kan tsadar mai da wutar lantarki
Majilisa ta ce babu wanda ya isa ya kara kudin mai da wutar lantarki. Hoto: NASS TV.
Asali: Facebook

Mene Majalisar ke cewa kan tsadar mai?

Shugaban Kwamitin Majalisar na yada labarai da hulda da jama'a, Yemi Adaramodu shi ya bayyana haka yayin hira da 'yan jaridu a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yemi ya ce su na kokarin dakile hakan ne ganin yadda matsalar man fetur da kuma basuka a bangaren wutar lantarki.

Idan ba a manta ba, Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan kudaden tallafin wutar ba.

Adelabu ya jingina matsalar ce da yawan basukan da ya yi yawa a kamfanonin wanda ya kai tiriliyan uku.

Matakin da Majalisar za ta dauka

Yemi ya ce:

"Kan matsalar tsadar man fetur, Majalisar ta kafa kwamitin da zai bincike ayyukan kamfanin NNPCL.

Kara karanta wannan

Aiki na shine na biyu mafi wahala a duniya, Gwamnan CBN Cardoso

"Yanzu muna jiran rahoton kwamitin wanda zai nuna shawara za mu bayar ko kuma tilasta bangaren zartarwa abin da ya kamata ta yi.
"Bangaren wutar lantarki kuma, Ministan zai iya cewa komai kan abin da ya shafi ma'aikatarsa, amma ba shi ne mai maganar karshe ba kan lamarin."

Yemi ya kara da cewa fadar shugaban kasa ta na tare da su inda ya ce yanzu rahoton kwamitin kawai suke jira don daukar mataki, cewar The Nation.

Ya ce Majalisa ta 10 ba za ta taba barin 'yan Najeriya ba saboda yin hakan kamar sun bar kansu ne inda ya ce sun zo ne ba don kansu ba illa don al'umma.

Adelabu ya bukaci cire tallafin wuta

Kun ji cewa ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya yi magana kan cire tallafin wutar lantarki a Najeriya.

Adelabu ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan kudaden tallafin wutar lantarki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel