Dan sanda a Yobe ya fashe da kuka, ya bayyana azabar da suke sha wurin Boko Haram

Dan sanda a Yobe ya fashe da kuka, ya bayyana azabar da suke sha wurin Boko Haram

  • Dan sandan Najeriya mai mukamin sajan dake aiki a Gujba ta jihar Yobe ya fashe da kuka yayin bayyana ukubar da suke sha a wurin Boko Haram
  • A wani bidiyo dake tashe a kafafen sada zumunta, an ga dan sandan na sanar da farmakin da aka kai musu aka kashe wasu abokan aikinsa
  • Ya koka da rashin kulawa da hukumomi ke nuna musu duk da wahalar da suke sha hannun miyagun 'yan Boko Haram

Wani dan sanda mai mukamin Sajan dake aiki a Gujba, jihar Yobe, ya zargi hukumomi da nuna musu halin ko in kula.

A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, jami'in dan sandan ya koka kan halin da yake ciki da kuma 'yan uwan aikinsa.

KU KARANTA: Jami'ar Kaduna ta koma karatu, ta bukaci iyaye su sa hannu kan wasu takardun alkawari

Dan sanda a Yobe ya fashe da kuka, ya bayyana azabar da suke sha wurin Boko Haram
Dan sanda a Yobe ya fashe da kuka, ya bayyana azabar da suke sha wurin Boko Haram. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara

Dan sandan mai mukamin sajan ya bada labarin yadda ya tsallake rijiya da baya daga hannun 'yan Boko Haram duk da hare-haren da suke kaiwa ya lamushe rayukan 'yan sanda masu yawa.

Ya ce 'yan ta'addan sun kona masa kadarori tare da ta sauran 'yan sanda a wani hari da suka sha da kyar, Daily Trust ta ruwaito.

Har yanzu dai babu tabbacin lokacin da aka nadi bidiyon amma a halin yanzu yana ta yawo a kafafen sada zumunta..

"Barkanku da safiya 'yan uwa 'yan Najeriya. Kun ga abinda ya faru da ni a Gujba, an kai mana hari a ranar 17 ga wata. Sun kashe min abokan aiki, sun kashe Paul. Kalle mu da muka sha da kyar, kalla abubuwanmu da suka kone.

“Tunda muka zo aiki jihar Yobe a watan Disamba, a yanzu wata bakwai kenan, babu abinci, babu alawus, babu komai. Saboda N53,000 da nake karba a matsayin dan sandan Najeriya mai mukamin sajan, ga ni nan zan mutu a jihar Yobe.

“Kalla yadda suka kone mana kaya. Kalla yadda jama'a ke mutuwa. Najeriya a duba matsalarmu, muna mutuwa babu mataimaki. A kan me muke mutuwa a kasar nan. Akwai Allah."

A wani labari na daban, bayan shekaru tara da majalisar wakilai ta rincabe da bincike kan wata damfarar tallafin man fetur, shugaban kwamitin wucin-gadi na wancan lokacin, Farouk Lawan, an yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan yari kan karbar cin hanci daga biloniya Femi Otedola, mamallakin daya daga cikin kamfanonin da ake bincika.

Wata babbar kotun tarayya dake zama a Apo wacce ta samu shugabancin mai shari'a Angela Otaluka a ranar Talata, ta kama Lawan da laifuka uku da ake zarginsa dasu tun a 2012, Daily Trust ta wallafa.

Wasu majiyoyi kusa da tsohon dan majalisar sun ce an tasa keyarsa zuwa gidan yarin dake Kuje a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel