A kasafin kudin 2022, Buhari ya bukaci N5.23bn na gyaran fadar shugaban kasa

A kasafin kudin 2022, Buhari ya bukaci N5.23bn na gyaran fadar shugaban kasa

  • A kasafin kudin shekarar 2022, za a kashe N5.231,101,743 wurin gyaran fadar shugaban kasa ta Aso Rock
  • Gine-ginen ofisoshin fadar shugaban kasan za su lashe N5,176,045,297, sai ginin gidaje za su ci N55,056,446 daga ciki
  • Gyaran da za a yi wa injinan wuta da wayoyin wutar lantarki za su kwashi N4,854,381,299 a kasafin kudin

Fadar shugaban kasa na bukatar kudi har N5.231,101,743 domin gyaran fadar shugaban kasa tare da gyaran wasu kadarorin da ke ciki a kasafin kudin shekarar 2022 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika gaban majalisar dattawa.

A duban da aka yi wa kasafin kudin, an gano cewa gyaran gine-ginen ofisoshi zai lamushe N5,176,045,297, yayin da ginen gidajen ciki zai kwashe N55,056,446 daga cikin N150,590,609,934 wanda fadar shugaban kasan za ta kashe, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2022: Fadar shugaban kasa za ta kashe N1.6bn wurin siyan sabbin ababen hawa

A kasafin kudin 2022, Buhari ya bukaci N5.23bn na gyaran fadar shugaban kasa
A kasafin kudin 2022, Buhari ya bukaci N5.23bn na gyaran fadar shugaban kasa. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

A kasafin kudin shekarar 2021, an ware N4,854,381,299 na gyaran injina da kuma kayan wuta a cikin fadar shugaban kasan.

A wannan gyaran da za a yi wa asibitin da ke cikin fadar shugaban kasan, ana tsammanin zai lashe kudi har N21,974,763,310, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda kiyasin ya nuna, gyaran ababen hawa da sassansu zai lashe kudi har N1.6bn idan aka alakanta shi da N436m wanda aka ware domin hakan a kasafin kudin shekarar 2021.

Kusan N180,089,000 aka ware saboda siyan tayoyin ababen hawan da harsasai ba su hudawa, motoci, ababen hawa CCU, manyan motocin daukar kaya, jifa-jifai, motocin asibiti da sauransu.

A shekarar da ta gabata, an ware kudi har N116,194,297 saboda hakan.

Sauya kayan sadarwa na fadar shugaban kasa a wannan shekarar zai lashe N400,000,000.

Kara karanta wannan

Terere: Yadda Fasto Oyedepo ya bude kamfani a kasar waje da sunan matarsa da 'ya'yansa

A kasafin kudin shekarar 2022, shugaban kasa Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo za su kashe N457,801,260 kan kayan abinci da kuma N301,138,860 da N156,662,400 na kudin cefanensu.

Buhari: Mu na da sabbin makaman yakar kowanne irin rashin tsaro

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar nan ta samu sabbin makamai da za ta iya yakar kowanne nau'in rashin tsaro, TheCable ta ruwaito.

Buhari ya sanar da hakan a ranar Asabar yayin bikin yaye daliban aji na 68 da suka hada da hafsoshin sojin kasa, ruwa da na sama da aka yi a makarantar horar da hafsoshin soji ta NDA da ke Kaduna.

Shugaban kasan ya bayyana damuwarsa kan rashin tsaro inda ya ce ya sakankance cewa sabbin kayan aiki da aka kawo za su matukar taka rawa wurin inganta tsaro a kasar nan, TheCable ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2022: N31m kudin man Janareton Aso Rock, N22.07m na Gas din girki, N33m na littafai

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng