Yan Sandan Jihohi: Hadimin Buhari Ya Shawarci Tinubu Ya Rushe Hukumomin Tsaro 2, Ya Fadi Dalilai

Yan Sandan Jihohi: Hadimin Buhari Ya Shawarci Tinubu Ya Rushe Hukumomin Tsaro 2, Ya Fadi Dalilai

  • Sanata Ita Enang ya shawarci Shugaba Tinubu ya ruguza hukumomin FRSC da kuma NSCDC kan matsalar tsaro
  • Enang wanda tsohon hadimin tsohon shugaban kasa ne, Muhammadu Buhari ya ce babu amfaninsu idan akwai ‘yan sandan jihohi
  • Sanatan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels inda ya ce dole a yi gagawar kirkirar ‘yan sandan jihohi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ba da shawarar rusa wasu hukumomi kan matsalar tsaro.

Sanata Ita Enang ya ce ya kamata Gwamnatin Tarayya ta ruguza hukumomin kula da hadura, FRSC da kuma hukumar NSCDC a kasar.

Kara karanta wannan

Zulum ya fatattaki shugaban sansanin 'yan gudun hijira kan wasu zarge-zarge, bayanai sun fito

Hadimin Buhari ya bai wa Tinubu shawarar rusa wasu hukumomin tsaro guda 2
Enang ya ce dole a rusa hukumomin NSCDC da FRSC a Najeriya. Hoto: Bola Tinubu, Ita Enang.
Asali: Facebook

Mene Enang ke cewa kan tsaron?

Enang wanda ya tsohon hadimin Buhari ne ya bayyana haka yayin hira da gidan talabiji na Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce hukumomion biyun ba su zama dole ba gagin yadda ake da yawan jami’an tsaro inda ya shawarci jami’an hukumomin guda biyu da a mayar da su jihohinsu don su yi aiki tare da ‘yan sandan.

Ya kuma ba da shawarar hade ‘yan sandan jihohin da wasu jami’an tsaron jihohi kamar su Amotekun da kuma Ebube-Agu.

Yayin da ke goyon bayan ‘yan sandan jihohi, Enang ya bukaci Tinubu ya umarci Atoni-janar na Tarayya ya shirya doka tare da mika ta ga Majalisa da gaggawa.

Wace shawara ya bayar kan tsaro?

A cewarsa:

“Bai kamata mu jira Majalisa sai ta kammala gyaran kundin tsarin mulki ba, bai kamata mu ba ta damar shiga wannan lamari ba.

Kara karanta wannan

Ribadu: Bayanai sun fito bayan kus-kus da Hadimin Tinubu yayi da Sanatoci a Majalisa

“Ya kamata Tinubu ya umarci Atoni-janar ya shirya doka tare da mika ta zuwa Majalisa wanda za a mata duba na musamman kan ‘yan sandan jihohi.”

Ya ce dole dokar ta fayyace iya ikon ‘yan sandan da kuma amfaninsu inda ya ce a baya ya ki amincewa da kudurin saboda tsoron gwamnoni za su yi amfani da hakan wurin cin zarafi.

Ya kara da cewa:

“Lokaci ya yi da ya kamata mu samar da ‘yan sandan jihohi, matsalar tsadar abinci da muke fama da ita duka rashin tsaro ke kawo wa.”

Tinubu ya amince da kirkirar ‘yan sandan jihohi

A baya, mun ruwaito muku cewa Shugaba Tinubu ya amince da samar da ‘yan sandan jihohi.

Tinubu ya amince da hakan ne bayan ganawa da gwamnonin jihohi kan samar da hanyar dakile rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel