‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 8 da Suka Yi Garkuwa da ‘Yan Makaranta a Jihar APC, An Kashe 1
- Jami'an 'yan sanda a jihar Ekiti sun yi nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane takwas tare da sheke daya daga cikinsu
- 'Yan bindigar da aka kama sune suka yi garkuwa da wasu yaran makaranta da malamansu a yankin Emure-Ekiti
- Haka kuma, 'yan ta'addan sune suka sace shugaban jam'iyyar APC, Hon. Paul Omotoso a cikin shekarar 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Ekiti - Rundunar 'yan sandan Ekiti ta ce ta kama masu garkuwa da mutane takwas wadanda suka sace yaran makarantar Apostolic Faith da malamansu a Emure-Ekiti, jihar Ekiti.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Adeniran Akinwale, ne ya gurfanar da masu garkuwa da mutanen a ranar Jumaá, 16 ga watan Fabrairu, a hedkwatar rundunar da ke Ado-Eikiti, rahoton Daily Trust.
Yadda aka kama 'yan bindigar da suka sace yaran makaranta a Ekiti
Akinwale ya ce an kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutanen yayin musayar wuta da jamián 'yan sandan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bayyana cewa guggun 'yan ta'addan sune suka sace shugaban jam'iyyar APC, Hon. Paul Omotoso a 2023.
Kwamishinan 'yan sandan ya ce:
"Binciken farko ya nuna cewa Sumo Karami, da mambobin kungiyarsa sune suka aiwatar da garkuwa da yaran makaranta da malamansu a Emure-Ekiti a ranar 29 ga watan Janairu.
"An samo wayar da aka yi amfani da ita wajen neman kudin fansa don sakin yara da malaman makarantar daga wajen wadanda ake zargin sannan kokarin da ake ta yi ne ya yi sanadiyar kamo mambobin kungiyar biyu a dajin Owo da ke jihar Ondo.
"An kwato abubuwa da dama daga wajensu da suka hada da bindigar AK-47, bindiga daya dauke da harsasai biyar, harsasan AK-47 guda 21 da sauransu."
Kwamishinan 'yan sandan ya yi kira ga al'umma da su dunga ba rundunar 'yan sandan hadin kai ta hanyar sanar da su muhimman bayanai da zai kai ga kama miyagu cikin gaggawa a jihar, rahoton Trust Radio.
'Yan bindiga sun farmaki Zamfara
A wani labarin na daban, mun ji cewa an kashe mutum bakwai yayin da wasu ƴan ta’adda suka yi garkuwa da wasu mutum kimanin 20 a wani hari da suka kai a jihar Zamfara.
Ƴan ta'addan sun kai harin ne da yammacin ranar Alhamis a ƙauyen Nasarawa Godel da ke ƙaramar hukumar Birnin Magaji ta jihar.
Asali: Legit.ng