Bayan Wike Ya Sanya Kyautar Miliyan 20, An Kama Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane a Abuja

Bayan Wike Ya Sanya Kyautar Miliyan 20, An Kama Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane a Abuja

  • Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya ta kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja, Saidu Abdulkadir
  • Shugaban 'yan bindigar ya shiga hannu ne yayin wani samame da jami'an rundunar suka kai sansaNin masu garkuwa da mutane
  • Hakan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sanya kyautar naira miliyan 20 ga duk wanda ya kamo masu satar mutanen da suka addabi birnin tarayyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Babban birnin tarayya, Abuja - Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama kasurgumin mai garkuwa da mutane, Saidu Abdulkadir.

Kwamishinan 'yan sandan birnin tarayya, CP Benneth Igwe, ya tabbatar da kamun Dahiru ga manema labarai a hedkwatar rundunar a ranar Juma'a, 16 ga watan Fabrairu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kwamushe mutum 5 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Arewa

'Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja
Bayan Wike Ya Sanya Kyautar Miliyan 20, An Kama Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane a Abuja Hoto: Hoto: @PoliceNG/ @TheNationNews
Asali: Twitter

CP Igwe ya ce bayan wani samame da suka kai kan sansanonin masu garkuwa da mutane a Nasarawa da Abuja ta yankin Kuje, da misalin tsakar daren Alhamis, 'yan bindigar sun yi arangama da jami'an yan sanda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan sanda suka kama mai garkuwa da mutane a Abuja

Ya ce 'yan ta'andan sun bude wuta ne a lokacin da suka hango jami'an tsaron, inda suka fafata da su ta hanyar musayar wuta, amma sai suka yi nasara a kansu.

Kwamishinan 'yan sanda ya ce:

“A ci gaban yakin da suke da masu aikata laifuka, jami’an ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja da ke sashin yaki da masu garkuwa da mutane, sun kai samame sansanonin masu garkuwa da mutane biyu.
"A kan iyakar Nasarawa da Abuja ta karamar hukumar Kuje a ranar 15/02/2024 da misalin karfe 12:00 na dare.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun kashe masallata 3 tare da sace wasu da dama a jihar Arewa

"Sun tarwatsa sansanin tare da kama wani Sa’idu Abdulkadir wanda aka fi sani da (Dahiru Adamu), wanda shi ne shugaban kungiyar kuma daya daga cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.
"Shine shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane da rundunar ‘yan sanda ta kama a ranar 14 ga Fabrairu 2024.”

An ceto mutum 2 daga sansanin 'yan bindigar

Ya kuma bayyana cewa an ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su, Habu Yakubu da Isufu Abubakar, wadanda aka sace daga kauyen Kwaita ta yankin Pegi na Kuje cikin koshin lafiya, rahoton Vanguard.

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewar:

"Binciken farko da rundunarmu ta gudanar ya bayyana cewa wanda ake zargin shine ya yi garkuwa da kashe hakimin garin Ketti a AMAC, Mista Sunday Yahaya Zakwai."

Wike ya sanya kyauta kan masu garkuwa da mutane

Lamarin na zuwa ne kwanaki bayan ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sanya tukuicin N20m kan wasu riƙaƙƙun masu garkuwa da mutane a birnin tarayya Abuja.

Masu garkuwa da mutanen dai ana zarginsu da hannu wajen kai hari tare da yin garkuwa da wasu jami’an tsaro biyu a wani sansanin sojoji da ke Abuja, cewar rahoton Leadership.

Asali: Legit.ng

Online view pixel