'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa Sun Halaka Mutum 7 da Sace Wasu da Dama

'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa Sun Halaka Mutum 7 da Sace Wasu da Dama

  • Wasu miyagun ƴan ta'adda ɗauke da muggan makamai sun aikata sabon aikin ta'addanci a jihar Zamfara
  • Ƴan ta'addan waɗanda suka kai harin cikin motoci sun salwantar da ran mutum bakwai tare da sace wasu mutum kimanin 20
  • Mazauna yankin sun koka kan yadda ƴan ta'addan suka kwashe sa'o'i da dama suna cin karensu babu babbaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - An kashe mutum bakwai yayin da wasu ƴan ta’adda suka yi garkuwa da wasu mutum kimanin 20 a wani hari da suka kai a jihar Zamfara.

Ƴan ta'addan sun kai harin ne da yammacin ranar Alhamis a ƙauyen Nasarawa Godel da ke ƙaramar hukumar Birnin Magaji ta jihar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun gano masana'antar kera makamai, sun cafke wanda ake zargi

'Yan ta'adda sun halaka mutane a Zamfara
'Yan ta'adda sun aikata sabon ta'addanci a Zamfara Hoto: @daudalawal
Asali: Twitter

Mutanen yankin da suka zanta da jaridar Premium times sun ce ƴan ta’addan sun zo ne a cikin motocin Toyota Hilux, saɓanin babura da suke hawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Wani mazaunin yankin mai suna Tukur Yusuf a safiyar ranar Juma'a ya bayyana cewa:

"Muna da gawarwaki bakwai a ƙidaya na ƙarshe. Wasu da dama sun samu munanan raunuka. Yawancin waɗanda aka sace mata ne. An jefa al’umma gaba ɗaya cikin ruɗani.
"Ƴan ta’addan waɗanda ake kyautata zaton ƴan tawagar Gwaska Dankarami ne, sun afka ƙauyen ne da misalin ƙarfe 6:00 na yamma cikin motocin ƙirar Hilux guda uku suka nufi hanyar fita daga cikin ƙauyen.
"Yana daga cikin tsare-tsarensu na yaudara. Lokacin da muka ga suna tuƙa mota zuwa hanyar Kasheshi Kura, ƙauyen da ke makwabtaka da mu, yawancin mu muna tunanin 'yan ta'adda za su kai hari a wani ƙauyen."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya fadi dalili 1 da ya sa tubabbun mayakan Boko Haram ba za su koma kashe-kashe ba

Ya ce sun zagaya ta hanyar waje inda suka fara harbi ba kakkautawa a lokacin da akasarin ƴan banga da ke ƙauyen suka fita domin taimakawa ƙauyen Kasheshi Kura.

Wani mazaunin garin wanda ya bayyana sunansa da Mubarak, ya ce an kashe abokinsa tun na yarinta a harin.

A kalamansa:

"Abin kunya ne yadda ƴan ta'adda za su shigo gari su fara harbin mutane. Sun yi tsawon sa’o’i uku ba tare da wanda ya kare mu ba.

Legit Hausa ta kasa jin ta bakin kakakin ƴan sandan jihar Zamfara Yazid Abubakar kan harin, saboda bai dawo sa amsar saƙon da aka tura masa ta wayarsa ba.

Ƴan Bindiga Na Lalata da Mata a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa miyagun ƴan bindiga sun koma yin fyaɗe ga mata da matan aure a yankin Tsafe na jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun koka kan yadda ƴan bindigan suka sauya salon gallazawa rayuwarsu, wanda hakan ya tilasta da yawa daga cikinsu yin ƙaura daga gidajensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel