Yan Sanda Sun Kwamushe Mutum 5 da Ake Zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne a Jihar Arewa

Yan Sanda Sun Kwamushe Mutum 5 da Ake Zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne a Jihar Arewa

  • Akalla mutum 5 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta kama a hanyar Bodinga zuwa Tambuwal
  • Rundunar ta bayyana cewa an kama mutanen ne dauke da bindigogi uku kirar AK-47 da kuma harsasai guda 90 da gidan harsasai uku
  • Hakazalika, a ranar 14 ga watan Fabrairu, misalin karfe 5:50 na yamma rundunar ta yi artabu da wasu 'yan biniga, inda ta kashe shida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Sokoto - Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta ce ta cafke wasu mutum biyar da take zargin 'yan dabar masu garkuwa da mutane ne da ke aiki a jihar.

An cafke wadanda ake zargin ne a ranar Talata 13 ga watan Fabrairu a babbar hanyar Bodinga zuwa Tambuwal da ke jihar.

Kara karanta wannan

Kano: An kama mutum 3 da laifin yin garkuwa tare da kashe wani yaro dan shekara 14

Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kama masu garkuwa da mutane a Sokoto.
Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kama masu garkuwa da mutane a Sokoto. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, TVC ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka kama sun amsa laifin su

ACP Adejobi ya ce an kama mutanen ne dauke da bindigogi uku kirar AK-47, harsasai guda 90 da kuma gidan harsasai na AK-47 guda uku.

Wadanda aka kaman su sun hada da Abdullahi Ali, Aliyu Mohammed, Abdullahi Umar, Aliyu Abdullahi da kum Mohammed Anas.

A yayin tuhumarsu, gaba dayan su sun amsa laifin da ake zargin su da aikata inda suka ce suna hanyar zuwa Tambuwal don yin garkuwa da wani.

A hanyar su ta kai harin ne tawagar rundunar 'yan sandan Najeriya ta jihar ta samu nasarar kama su.

Yan sanda sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a Sokoto

Gidan talabijin na NTA ya ruwaito cewa, a ranar 14 ga watan Fabrairu, misalin karfe 5:50 na yamma, an ga gilmawar wasu 'yan bindiga a kauyen Gigane, jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Bayan cafke tsohon soja, Ma'aikacin jinya mai bai wa yan bindiga kulawa ya shiga hannu, ya yi magana

Sashen kar farmaki na rundunar 'yan sandan jihar sun farmaki 'yan bindigar inda aka yi dauki ba dadi a tsakanin su.

A yayin artabu ne aka kashe 'yan bindiga shida tare da kwace bindiga kirar GPMG da kuma harsasai shida.

Ya zuwa yanzu dai jami'an tsaro na ci gaba da matsin lamba kan 'yan bindiga da ma masu aikata laifi don kakkabe su daga jihar.

Yan bindiga sun kashe dan takarar majalisar wakilan PDP

A wani labari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani tsohon dan majalisar tarayya.

Lamarin ya faru a karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra, inda 'yan bindigar suka fara yin garkuwa da Jude Oguejiofor tare da dan uwansa.

An ruwaito cewa sun kashe Oguejiofor amma sun saki dan uwansa, lamarin ya sa zuciyar mahaifin dan siyasar ta buga ya mutu nan take

Asali: Legit.ng

Online view pixel