Yadda Jami’an Yan Sanda Suka Yi Garkuwa da Wani Mazaunin Abuja, Suka Kwashe Gaba Daya Kudin Asusunsa

Yadda Jami’an Yan Sanda Suka Yi Garkuwa da Wani Mazaunin Abuja, Suka Kwashe Gaba Daya Kudin Asusunsa

  • Rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wasu daga cikin jami'anta da ake zargi da yin garkuwa da wani dan kasuwa a Abuja
  • Dan takarar jam'iyyar LP a zaben 2023, Harrison Gwamnishu ya fara fitar da labarin yin garkuwa da dan kasuwar
  • Gwamnishu ya ce 'yan sandan su tilasta mutumin tura masu naira miliyan 29.9 tare da yi masa barazana kafin suka sake shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A yayin da ake ta fama da matsalar tsaro a Abuja, an kama wasu jami’an ‘yan sanda bisa zargin karbar naira miliyan 29.9 da karfin tsiya daga hannun wani mazaunin birnin.

Lamarin, a cewar Harrison Gwamnishu, dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, ya faru ne a watan Janairu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da gobara ta kashe yaro dan shekara 4 a Jihar Kano

Yan sanda sun yi garkuwa da wani dan kasuwa a Abuja
Harrison Gwamnishu ya kai kwarmaton jami'an 'yan sanda da suka yi garkuwa da wani a Abuja. Hoto: @HarrisonBbi18
Asali: Twitter

Sun tatike asunsun bankinsa

Gwamnishu ya bayyana hakan a wani cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce jami’an ‘yan sanda sun yi garkuwa da dan kasuwar a Abuja inda suka tsare shi har sai da ya tura musu dukkan kudaden da ke cikin asusun bankinsa.

Daga nan ne kuma suka tilasta shi ya kira ‘yan uwa da abokan arziki su ci gaba da aika masa kudi yana basu kafin su sake shi.

An kama wasu daga cikin jami'an

Ya kuma yi zargin cewa 'yan sanda sun kama mutumin ne ba tare da wani dalili ba, inda ya ce jami’an ‘yan sandan ba su nemi ya rubuta wani jawabi ba.

Gwamnishu ya wallafa hotunan shaidar tura kudaden tare da bidiyon da ya wallafa.

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

Da yake tsokaci kan wannan bidiyo a ranar Talata, kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar da kama wasu daga cikin masu laifin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rundar 'yan sanda na neman jami'inta ruwa a jallo

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta bayyana cewa tana neman daya daga cikin jami’an rundunar, Sufeta Audu Omadefu bisa zargin kisan kai.

Ikenga Tochukwu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata.

Kakakin ‘yan sandan ya ce za a iya gane ma’aikacin Omadefu da ya gudu ta lambar aikinsa ta AP 362178.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel