Kano: An Kama Mutum 3 da Laifin Yin Garkuwa Tare da Kashe Wani Yaro Dan Shekara 14

Kano: An Kama Mutum 3 da Laifin Yin Garkuwa Tare da Kashe Wani Yaro Dan Shekara 14

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutum uku da ake zargin sun kashe wani karamin yaro bayan yin garkuwa da shi
  • Kakakin rundunar jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun nemi naira miliyan 4 kudin fansa
  • Bayan da aka kama su ne suka amsa laifin tare da fadin inda suka jefar da gawar yaron a kauyen Sabuwar Za da ke jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun kama wasu mutane uku da ake zargin sun yi garkuwa tare da kashe wani yaro dan makwabcinsu mai shekaru 14.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdulahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar ta fara samun rahoto daga wani Alhaji Rabiu Abdullahi na Hotoron Fulani Quarters Kano.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kwamushe mutum 5 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Arewa

Kano: An kama mutum 3 da laifin yin garkuwa tare da kashe wani yaro dan shekara 14
Kano: An kama mutum 3 da laifin yin garkuwa tare da kashe wani yaro dan shekara 14. Hoto: @KanoPoliceNG
Asali: Twitter

Abdullahi ya shaida cewa an kira shi a waya cewa an yi garkuwa da dansa Abdullahi Sani kuma ana bukatar ya biya kudin fansa naira miliyan hudu domin a sako shi, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun kama wadanda ake zargi

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya ba ‘yan sandan sashin yaki da garkuwa da mutane umarnin ceto yaron tare da kamo masu laifin.

Kiyawa ya ce, nan take rundunar ta dauki matakin da ya sa aka kama jagoran wadanda ake zargin, Ismail Adamu a unguwar Hotoron Fulani Quarters, Kano.

Ya bayyana cewa Adamu ya amsa laifin hada baki da wani Risi na Mariri Quarters Kano domin yin garkuwa da wanda aka kashe, Leadership ta ruwaito.

An gano inda masu laifin suka wurgar da gawar yaron

Kara karanta wannan

Bayan cafke tsohon soja, Ma'aikacin jinya mai bai wa yan bindiga kulawa ya shiga hannu, ya yi magana

“Sun bayyana cewa sun tafi da yaron zuwa kauyen Sabuwar Zara inda suka daba masa wuka a wuyan sa, suka jefa shi a cikin wani rami.
"Daga baya kuma suka tuntubi mahaifin yaron tare da neman ya basu naira miliyan 4 don su sako shi."

- A cewar Kiyawa

Binciken da rundunar ta yi ya kai ga an kama wasu mutane biyu; Musa Usman da Abdullahi Usman wadanda ke da hannu wajen aikata laifin.

Kiyawa ya ce wadanda ake zargin za su gurfana a gaban kuliya da zarar rundunar ta kammala bincike.

Mummunar gobara ta babbake ofishin 'yan sandan Kano

A wani labarin daga jihar Kano, Legit Hausa ta ruwaito cewa wuta ta tashi a ofishin 'yan sanda na karamar hukumar Nasarawa da ke jihar Kano.

Gobarar ta lakume wasu sassa na ofishin, amma hukumar kashe gobara ta yi nasarar shawo kanta tare da ceto wasu kadarorin.

Sai dai har yanzu ba a iya gano abin da ya haddasa gobarar ba amma rundunar ta ce wutar ba ta shafi sashen ajiyar makamanta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel