Bayan Cafke Tsohon Soja, Ma'aikacin Jinya Mai Bai Wa Yan Bindiga Kulawa Ya Shiga Hannu, Ya Yi Magana

Bayan Cafke Tsohon Soja, Ma'aikacin Jinya Mai Bai Wa Yan Bindiga Kulawa Ya Shiga Hannu, Ya Yi Magana

  • Kwana daya bayan kama tsohon soja a Kaduna, an sake cafke wani ma'aikacin jinya da ke kula da 'yan bindiga a Sokoto
  • Wanda ake zargin, Jamilu Yusuf mai shekaru 35 ya tabbatar da laifin da ake zarginsa da aikatawa na jinyan 'yan ta'adda
  • Kwamishinan 'yan sanda, Ali Kaigama shi ya gabatar da su inda ya ce Jamilu ne mai bai wa 'yan ta'addan kulawa idan sun samu rauni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Rundunar 'yan sanda a jihar Sokoto ta yi nasarar cafke wani da ke kulawa da 'yan bindiga idan sun samu raunuka.

Wanda ake zargin, Jamilu Yusuf mai shekaru 35 an kama shi ne a yankin Badon Hanya da ke birnin Sokoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun kashe masallata 3 tare da sace wasu da dama a jihar Arewa

'Yan sanda sun kama mai kula da 'yan bindiga idan sun ji rauni
Ma'aikacin Jinya da Ke Bai Wa 'Yan Bindiga Kulawa Ya Shiga Hannu a Sokoto. Hoto: Ahmed Aliyu.
Asali: Twitter

Mene ake zargin Jamilu da aikatawa?

Jamilu wanda ma'aikacin jinya ne an kama shi da wasu mutane 12 akan hanyarsu ta zuwa Tambuwal don gudanar da wani aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Ali Kaigama shi ya gabatar da wadanda ake zargin inda ya ce Jamilu ne mai bai wa 'yan ta'addan kulawa idan sun samu raunuka.

Kaigama ya ce sun yi nasarar kwacen bindigu kirar AK-47 guda uku da alburusai da dama a hannun wadanda ake zargin.

Wanda ake zargin ya tabbatar da zargin

Da ake tuntubarsa, Yusuf ya tabbatar da aikata laifin da ake zarginsa a kai inda ya ce yana bai wa 'yan bindigar kulawa.

Ya tabbatar da cewa duk lokacin da wani daga cikinsu ya samu rauni idan ya yi masa magani su na biyansa fiye da dubu dari.

Kara karanta wannan

"Ya dauki nauyin kawunnai na 10 zuwa Hajji": Tambuwal ya tuna haduwarsu ta karshe da Wigwe

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan cafke wani tsohon soja da ke safarar kayan sojoji ga Bello Turji a Zamfara.

An kama tsohon soja kan alaka da Bello Turji

A baya, mun labarta muku cewa 'yan sanda sun yi nasarar cafke wani tsohon sojan sama da ake zargi da kai wa Bello Turji kayan sojoji.

Wanda ake zargin, Ahmed Mohammed Tsohon soja ne wanda aka kore shi a aiki bayan shafe shekaru biyar ya na aikin.

Ahmed ya tabbatar da cewa shi ya ke kai wa Bello Turji kayan sojoji da sauran 'yan ta'adda da suka addabi jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel