Kano: Yayin da Ake Cikin Matsin Tsadar Rayuwa, Gwamnati Za Ta Dauki Mataki Kan Masu Boye Abinci

Kano: Yayin da Ake Cikin Matsin Tsadar Rayuwa, Gwamnati Za Ta Dauki Mataki Kan Masu Boye Abinci

  • Shugaban hukumar yaki da cin hanci a Kano, Barista Muhuyi Magaji ya sha alwashin kai samame wasu wurare da ake boye abinci
  • Rimin Gado ya ce za su fara kai ziyarar ce don zakulo wadanda ke boye a binci tare da siyar da kayan abincin ga jama'ar gari
  • Muhuyi Magaji ya bayyana haka ne a yau Alhamis 8 ga watan Faburairu a birnin Kano yayin da jama'a ke cikin wani hali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Shugaban hukumar korafe korafe da yaki da cin hanci a jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji zai fara kai samame inda ake ajiyar kayan abinci.

Muhyi ya ce za su fara kai ziyarar ce don zakulo wadanda ke boye a binci tare da daukar mataki a kansu.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon APC ya gaji da tsarin Tinubu, ya nemi a sake zama kan tsare-tsaren gwamnati

Shugaban hukumar ya bayyana haka ne a yau Alhamis 8 ga watan Faburairu a birnin Kano.

Gwamnatin Kano za ta kai samame runbunan abinci yayin da ake cikin wani hali
Hukumar yaki da cin hanci ta gargadi masu boye abinci a Kano. Hoto: Muhuyi Rimin Gado, Business Trumpet.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane gargadi Muhuyi ya yi a Kano?

Rimin Gado ya yi wannan barazana ce yayin da ake cikin wani yanayi na mawuyacin hali a Najeriya.

Shugaban hukumar ya ce duk wanda suka samu da boye kayan za su fito da abincin tare da siyar da shi ga jama'a.

Ya ce haramun ne kuma karya dokar kasa ce boye abinci lokacin da mutane ke cikin tsanananin wahalar abinci a kasa.

Ya bayyana wurin da za su fara kai samame

Daily Trust ta tattaro cewa za a fara kai samamen ne wuraren da ake zargi an boye kayan abinci ne kafin watan Azumin Ramadan.

Ya kara da cewa wurin da zasu fara dira shi ne Kasuwar Dawanau inda yace duk wanda aka kama ya boye abinci za a fito da abincin a kai kasuwa.

Kara karanta wannan

Mahara sun sake hallaka fitaccen basarake a jihar Arewa, bayanai sun fito

Har ila yau, Magaji ya ce hakan zai taimaka wurin sauko da farashin kayan abinci a jihar da ma kasa baki daya.

Kotu ta bai wa Tinubu wa'adin kwana 7

Kun ji cewa kotu ta umarci Shugaba Tinubu ya kawo karshen tsadar rayuwa a kasar nan da mako daya.

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin wani irin mawuyacin hali tun bayan cire tallafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel