Kano Za Ta Amfana Sakamakon Haduwar Gwamna Abba da Jakadan Kasar Kanada

Kano Za Ta Amfana Sakamakon Haduwar Gwamna Abba da Jakadan Kasar Kanada

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf da jami’an gwamnatin Kano sun hadu da Jakadan Kanada a gidan gwamnati
  • Kasar Kanada ta yarda ta taimakawa Jihar Kano domin magance matsalolin kiwon lafiya, ilmi da sauransu
  • Abba Kabir Yusuf ya samu za a farfado tsohuwar alakar da ke tsakanin gwamnatin Kano da Kanawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Gwamnatin Kano ta nemi agajin kasar Kanada domin magance wasu daga cikin matsalolin da suka addabi jihar.

Mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da haka a shafin X bayan ganawa da ya yi da Jakadan Kanada a Najeriya.

Abba. Kano.
Gwamnan Kano da Jakadan Kanada Hoto: @KYusufAbba
Asali: Twitter

Jakadan Kanada a garin Kano

Mr. Jamie Christoff ya yi zama da gwamnan Kano a gidan gwamnati a ranar Talata. Rahotonmu ya kawo amfanin haduwar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zage yayi karin albashi, ma’aikatan Jihar sun raina N10, 000 a wata 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban wakilin kasar ketaren a Kano ya bayyana cewa ana fama da matsalolin da suka bukaci taimakon gwamnatinsu.

Duk da kokarin gwamnatin jihar, The Guardian ta rahoto Jamie Christoff yana cewa sai sun dafa a kananan hukumomi 44.

Kokon barar Gwamna Aba Kabir Yusuf

"Mu na da wasu kalubale na muhalli da yanayi da mu ke bukatar gwamnatin Kanada ta tallafawa jihar Kano."
"Kano saboda kusancinta da hamadar sahara tana fuskantar manyan kalubale musamman fari, zaizayewar kasa da ambaliya a duka kananan hukumomi 44 da ke jihar."

- Abba KabirYusuf

Kano da noman rani a Najeriya

Rahoton VON ya ce Mai girma gwamna ya yabi hobbasan Kanada wajen habaka noma wanda sun fi kowa noman rani a kasar.

Gwamnan da aka fi sani da Abba Gida Gida ya mika kokon bararsu domin inganta harkar kiwon lafiya domin taimakawa jama’a.

Kara karanta wannan

Ramadan: Abba ya zauna da ‘yan kasuwan Kano, ya roki a fito da abinci da aka boye

Ilmi zai samu karin gata a Kano

A jawabinsa, gwamnan Kano ya yi bayanin yadda jihar tayi nisa a noman rani, yake cewa suna da dam har 22 da ake amfana da su.

A bangaren ilmin zamani, Abba ya ce kasar ketaren za ta farfado da tallafin da ta saba a mutanen Kano tun farkon shekarun 1980s.

An ga Abba yana yi wa Christoff da ‘yan rakiyarsa sallama bayan tattaunawr da suka yi.

Shari'ar Abba Kabir Yusuf

A baya an rahoto Kakakin jam’iyyar NNPP na kasa ya zargi kotu da sakin hanya a shari’ar Kano, ya ce an nemi a zalunci Kanawa.

Oladipupo Olayokun yake cewa da frko Nasir Gawuna ya taya Abba Kabir Yusuf nasara a 2023, amma aka nemi canza labari a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng