Hatsabibin ‘Dan Bindiga da Ya Addabi Jihar Arewa, Kachalla Duna, Ya Shiga Hannu

Hatsabibin ‘Dan Bindiga da Ya Addabi Jihar Arewa, Kachalla Duna, Ya Shiga Hannu

  • Dakarun tsaro sun yi gagarumar nasara a kokarin da suke na kakkabe 'yan ta'adda da miyagu a fadin kasar nan
  • Wani hatsabibin 'dan bindiga da ya addabi al'umma a garuruwan Sokoto, Kachalla Duna Tagirke, ya shiga hannu
  • Kachalla Duna na aiwatar da hare-harensa ne da goyon bayan kasurgumin 'dan ta'adda, Bello Turji a yankin gabashin Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Rahotanni sun kawo cewa dakarun tsaro a jihar Sokoto sun yi nasarar kama wani hatsabibin 'dan bindiga, Kachalla Duna Tagirke.

Mai fashin baki kan harkokin tsaro, Zagaloza Makama ne ya sanar da labarin kamun Kachalla a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

Dakarun tsaro sun kama hatsabibin 'dan bindiga
Hatsabibin ‘Dan Bindiga da Ya Addabi Jihar Arewa, Kachalla Duna, Ya Shiga Hannu Hoto: @HQNigerianArmy, @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Zagazola ya bayyana cewa 'dan ta'addan da aka kama ya yi kaurin suna wajen addabar garuruwa da dama a jihar Sokoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, ya ce Duna Tagirke na aiwatar da ta'asarsa ne da taimakon kasurgumin 'dan ta'adda, Bello Turji.

An tattaro cewa jami’an tsaro sun yi nasarar aiwatar da aikin damke Kachalla bayan samun bayanan sirri kan inda yake a yankin gabashin Sokoto.

Me yan Najeriya ke cewa kan kamun Kachalla Duna?

@DavinJavin ya yi martani:

"Jinjina ga rundunar sojin Najeriya, kwamakin Bello Turji kirgaggu ne."

@jogana05 ya yi martani:

"Me yasa mutumin nan ke shakar iskarmu har yanzu? Ku sheke shi mana."

@exboy10 ya ce:

"Guru da laya sun ki su yi aiki."

@Sadiq_ibrahim1 ya ce:

"Ya kamata a yanke masa hukunci irin wanda yake yi wa wadanda suka shiga hannunsa."

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka kama masu laifi 400 a jihar APC

@Ajagbemayor94 ya ce:

"Babu amfanin murna saboda gwamnati za ta sake shi a gobe saboda ya yi rantsuwa da littafi mai tsarki."

@Yulimanne ya yi martani:

"Labari mai dadi!"

@AbubakarTk ya ce:

"Allah ya ci gaba da tona masu asiri da masu daukar nauyin su."

Gwamna Zulum ya fadi makarin 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Borno karkashin Gwamna Babagana Umaru Zulum ta bayyana muhimmin abubuwan da suka karya lagon ƴan ta'adda a jihar.

Kwamishinar harkokin mata da walwala, Hajiya Zuwaira Gambo, ta ce mutuwar Abubakar Sheƙau, na ɗaya daga cikin abiɓda ya sa ƴan ta'addan suka ja da baya.

Idan baku manta ba, Shekau, shugaban Boko Haram ya bindige kansa har lahira lokacin da mayaƙan ISWAP da suka takun saƙa suka farmaki sansaninsa a dajin Sambisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng