ASUU Ta Firgita Shugaba Tinubu, An Fara Jin Kanshin Yajin-Aiki a Jami’o’in Gwamnati

ASUU Ta Firgita Shugaba Tinubu, An Fara Jin Kanshin Yajin-Aiki a Jami’o’in Gwamnati

  • Kungiyar malaman jami’a ta zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawuran da ta dauka na tsawon shekara da shekaru
  • Shugaban ASUU na kasa baki daya ya zanta da manema labarai bayan taron NEC da malaman suka shirya kwanaki
  • Farfesa Emmanuel Osodeke ya jero sabaninsu da gwamnati, yake nuna za su iya yajin-aiki saboda hana su hakkokinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kungiyar ASUU ta fara nuna cewa batun rashin cika alkawarin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu yana tada mata hankali.

Shugaban kungiyar malaman jami’a na kasa, Emmanuel Osodeke, ya bayyana wannan da kan shi, Punch ta kawo labarin nan.

ASUU.
ASUU: Malamai da daliban jami'a Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Emmanuel Osodeke ya zanta da manema labari a birnin Umuahia da ke jihar Abia a ranar Laraba bayan taron NEC da ASUU ta yi.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ASUU ta yi taron NEC a jami'ar Delta

Malaman jami’an na ASUU sun yi zaman majalisar kolin a jami’ar jihar Delta a karshen makon jiya, a nan aka tattauna batutuwa.

Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce sun yi nazarin yarjejeniya da duk zaman da suka yi da gwamnatocin jihohi da na tarayya a can baya.

Yarjejeniyar kungiyar ASUU da gwamnati

Abubuwan da ASUU ta duba sun hada da yarjejeniyar 2009, zancen IPPIS, bashin albashin watanni sai kuma alawus na ECA.

This Day ta ce malaman suna kukan yadda aka sauke shugabannin da ke kula da jami’o’i, matsalar TETFund, rashin kudin aiki.

ASUU ta na kokarin ganin gwamnatoci sun inganta ilmi, wannan ya kai ta yajin-aiki kamar yadda NLC ta TUC su ke shirin shiga.

ASUU ta ce malamai na cin kwa-kwa

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

Farfesan ya ce NEC ta tsorata da labaran da ta ke samu game da malaman jami’an da suka mutu ko su ke cikin mummunan yanayi.

A dalilin wahalar aikin koyarwa a jami’o’i ne ASUU ta ce malaman sun shiga matsala domin gwamnati ta gagara cika alkawuranta.

Farfesa Osodeke yana mamakin yadda gwamnati ke neman hana su albashinsu har sai sun koma yajin-aiki kamar yadda aka saba.

ASUU, IMF da gwamnatin tarayya

A karshen jawabinsa, shugaban ASUU ya bada shawarar gwamnati tayi watsi da shawarwarin bankin Duniya da hukumar IMF.

Kwanan nan aka samu labari Najeriya ta cigaba da biyan tallafin da Shugaba Bola Tinubu ya cire a kan man fetur a Mayun bara.

Masana a hukumar IMF sun zargi Gwamnatin tarayya da biyan kudi domin a hana fetur tashi, sun bada shawarar watsi da tsarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel