Sabuwar Kungiyar Masu Tada Kayar Baya ta Bullo a Najeriya, Tana Barazana ga Zaben 2023

Sabuwar Kungiyar Masu Tada Kayar Baya ta Bullo a Najeriya, Tana Barazana ga Zaben 2023

  • Sabuwar kungiyar ‘yan tada kayar baya mai suna The Force of Egbesu, ta bullo a yankin kudancin Najeriya a jihar Bayelsa tana barazana kan hana zabe
  • Kungiyar ta koka kan cewa an yi watsi da su don haka Shugaba Buhari da Gwamna Diri su zo su tattauna kafin su fara tafka tsiya
  • Shugaban kungiyar masu tada kayar bayan ya sanar da cewa matukar ba a yi musu abinda suke so ba, ba za su bari a yi zaben 2023 ba kuma ba barazana suke ba

Bayelsa - Wata sabuwar kungiyar ‘yan tada kayar baya mai suna The Force of Egbesu, ta bayyana a yankin Neja Delta inda ta yi jan kunne da kakkausar murya ga Shugaba Buhari da gwamnonin jihohi da su yi abinda ya dace don walwalar yankin ko kuma su balle rashin kyautawa yayin zaben watan Fabrairu a yankin, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kamfen zub da jini: An sheke wani, da dama sun jikkata a kamfen PDP a wata jihar APC

Taswirar Bayelsa
Sabuwar Kungiyar Masu Tada Kayar Baya ta Bullo a Najeriya, Tana Barazana ga Zaben 2023. Hoto daga vanguardngrnews.com
Asali: UGC

A wani sako da bidiyo da aka fitar a kwanakin karshen mako, shugaban kungiyar da ya bayyana sunansa da Janar Gbolodi, ya koka kan yadda aka yi watsi da shi da kungiyarsa tun 2010 kuma aka watsar da yankin Bashan mai arzikin man fetur a Neja Delta.

Takardar tace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ina kira ga shugabannin PDP da APC da basu son cigaban yankin da su hanzarta yin gyara kafin lokaci ya kure. Ina son kira ga shugabannin siyasa musamman na PDP da APC a jihar Bayelsa kan cewa Bashan na da arzikin man fetur amma babu cigaba, har yanzu a baya ta ke.
“Sun gaza a dukkan alkawuran da suka mana, nayi aiki da PDP da APC a jihar amma sun gaza cika alkawuransu, sun gaza a yankina.
“Ina aike wannan sakon ga shugaba Buhari da Gwamna Douye Diri, idan ku na son magance rashin adalcin da aka yi mana, ku zo mu tattauna. Amma idan ku ka ki, za mu zo mu ku, ba za a yi zabe a Bashan ba da sauran yankuna.

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

“Muna jiran fahimtarku, muna jiran martanin ku kan kokenmu da yadda ku ka yi watsi da mu.
“Idan kuma yafi mu ku ku yi amfani da karfi a kan mu, mun shirya yaki, ba mu jin tsoron Fir’auna da ku ke da shi kuma muna jiran wadanda za ku aiko. Mun san cewa mutuwa dole ce ga kowa, mun shirya yaki.
“Idan kun gaza zuwa wurinmu kafin zabukan Fabrairu, ba za a yi zabe a Bashan ba d ke kudancin karamar hukumar Ijaw da sauran yankuna. Ku sani cewa ba barazana bace kawai.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel