Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci zaman bude taron AU karo an 30
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya halarci zaman buda taron shugabannin kasashen Afrika karo na 30 a yau Lahadi, 28 ga watan Junairu, 2018.
Jaridar Legit.ng ta samu wannan labari ne daga shafin sada zumuntar babban mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, inda yace:
“Shugaba Buhari tare da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo da tsohon shugaban gwamnatin soja, Abdulsalami Abubakar; ministan sufurin jihar sama, Hadi Sirika, ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama; ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN a zaman bude taron shugabannin kasashen Afrika karo da 30 a birnin Adidss Ababa, kasar Ethiopia”.
Mun kawo rahoto cewa bidiyo ta bayyana a yau inda shugaba Buhari ke tattaunawa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, gabanin fara taron.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng