Najeriya ta mallaki Dala Biliyan 41 na kudin kasar waje – CBN

Najeriya ta mallaki Dala Biliyan 41 na kudin kasar waje – CBN

- Kudin kasar wajen Najeriya ya haura Dala Biliyan 41

- A farkon shekarar nan CBN na da Dala Biliyan 38.91

- Ana sa rai kafin karshen bana a samu Dala Biliyan 50

Babban bankin Najeriya na CBN ya bayyana cewa kudin kasar wajen da Najeriya ke da shi ya karu zuwa sama da Dala Biliyan 41 wannan karo. A kusan mako guda Najeriya ta hada abin da ke nema ya kai Dala Miliyan 500.

Najeriya ta mallaki Dala Biliyan 41 na kudin kasar waje – CBN

Kudin kasar wajen Najeriya ya haura Dala Biliyan 41

Labarin da mu ke ji ba da dadewa ba a cikin kasar shi ne, Bankin na CBN ya samu karin Dala Miliyan $442.8 a cikin kwanaki 6. Hakan dai na nufin a dare guda kudin da Najeriya ta mallaka na kasar waje ya tashi da sama da kashi 1%.

KU KARANTA: An nemi Makarfi ya tsaya takarar Shugaban kasa a 2019

Idan ba ku manta ba dai a farkon hawan Shugaba Buhari kudin kasar wajen da Najeriya ta adana sai da ya sauka kasa. Yanzu dai kudin sun yi wani irin babbakowar da su taba yi ba tun a karshen shekarar 2014 lokacin mulkin PDP.

Jaridar Leadership ta kasar nan tace rabon da kudin da ke asusun Najeriya su yi irin yawan da su kayi wannan karo tun a Disamban 2013. Ana sa rai kafin karshen wannan shekarar, Najeriya za ta mallaki abin da ya haura Dala biliyan 50.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel