Miyagun Kwayoyi: Tramadol tafi kowacce kwaya hadari a duniya

Miyagun Kwayoyi: Tramadol tafi kowacce kwaya hadari a duniya

- Ana sayar da muggan magunguna ga matasa a yankin arewa kamar ba laa-haula

- Magungunan suna da muguwar illa kuma ga uwar tsada

- An ganio Tramadol yafi kowanne illa cikinsu

Miyagun Kwayoyi: Tramadol tafi kowacce kwaya hadari a duniya

Miyagun Kwayoyi: Tramadol tafi kowacce kwaya hadari a duniya

Kwayar Tramadol da matasa ke sha da sunan jin dadi tafi kowacce kwaya hadari, inji masana. Kwayar tana da sinadarin cocaine ne wanda ake amfani dashi a da don rage zai ko radadin ciwo, da kawo dan farin ciki ko nishadi na dan wucin gadi.

Sai dai maras lafiya ake baiwa a lokuta da kayyadajjen adadi, amma sai abin ya basu tsakanin masu son maye. Inda suke kashe makudan kudi wajen shan wadannan kwayoyi domin buguwa.

A kimiyyance, an gano cewa kwakwalwa takan so ta warware wasu takaicin na rayuwa, inda a lokuta da dama rashin abin yi da rashin kudi kan jawo su. A wasu yankunan duniya, kamar wajen Turawa, giya suke sha su huce takaicinsu, wanda take da illa ga hankali na wucin gadi, kuma takan auri mutum har ya zama dan-giya, ko barasa.

A yankunan da an haramta irin wadannan kayan maye, kamar su wiwi da giyar, sai samari suka koma shan abinda baza'a ce sun aikata haramun ba. Sai dai matsalar, maimakon giya da aka iya gani sanda mutum ya saya a kayyade masa, wadannan kwayoyi a boye ake shansu babu kuma likita.

DUBA WANNAN: Shehu Sani da Elrufai- fadan karshe

Don haka sai abin ya zama annoba ga arewacin Najeriya, da yankunan larabawa. Wanda kuma aka gano Tramadol din yafi kowanne illa.

Yawanci kasashen Asiya su ke hada wadannan kwayoyi, amma tunda su kudi kawai suke nema, kuma sun kula akwai kasuwar magungunan a nan, sai kawai a su yi ta antayo mana mu kuwa muyi ta sha muna zarewa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel